Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar

  • Gwamnatin Katsina ta fitar da sabon tsarin kalolin fentin motocin haya a jihar
  • Wannan na daga cikin matakan tabbatar da tsaro da gwamnatin ke dauka, cewar kwamishanan sufuri
  • Wannan ya biyo bayan dokar hana hawa ababen hawa a wasu garuruwa

Katsina - Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da samfurin sabbin kalolin fentin da ake son masu ababen hawan haya suyi wa motoci da kurkurorinsu (Keke Napep).

Majalisar zartarwar jihar Katsina ta amince da wannan sabon tsari ne a zaman da tayi na karshe a dakin taro na Gidan Janar Muhammadu Buhari.

Majalisar ta amince da irin kalolin fentin da za a yiwa ababen hawan.

Kalolin dai sune kalar dorowa da kuma kalar bula.

Bayan haka, za'a fitar da tsarin sanyawa kowace mota lamba ta musamman da za ta banbancesu bisa kananan hukumomin da suka fito.

Kara karanta wannan

Sabuwar doka: Gwamnatin jihar Jigawa ta sanya dokar hana babur a fadin jihar

Kwamishinan Ayyuka da gidaje na jihar Katsina ya bayyana hakan a yayin zama da akayi da manema labarai, rahoton Katsina Post.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara cewa hakan duk yana cikin kokarin tsare lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar nan.

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar
Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar Hotuna: Katsina Post
Asali: Facebook

A rika lura da sa ido kan masu kaiwa yan bindiga bayanai

Haka kuma, gwamnatin jihar ta ja hankalin al’umma da suka sa ido sosai wajen gano bata garin cikin mu da suke aike ma ‘yan ta’adda da bayanai domin hadarin su yafi na masu ta’addancin.

Mai ba Gwamna Shawara a kan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina ya bada tabbacin cewa ba za'a daina aikin da aka fara a kananan hukumomin Jibia da Batsari ba sai an tabbatar da an kakkabe ‘yan ta’addar da suka addabi al’umma.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Kaduna ta haramta safarar dabbobi daga wasu jihohi

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar
Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar Hoto: Katsina Post
Asali: Facebook

An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

An toshe hanyoyi sadarwa na zamani a kananan hukumomin jihar Katsina akalla 13 a yau Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021.

Wannan sabon abu ba zai rasa alaka da artabun da jami'an tsaro ke yi da yan bindiga a yankin Arewa maso yamma ba.

Kananan hukumomin da wannan abu ya shafa sun hada da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da Kurfi, Funtua, Bakori da Malumfashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel