Hukumar ICPC ta kwato garkame kadarori da dan majalisar Yobe ya boye na mazabarsa

Hukumar ICPC ta kwato garkame kadarori da dan majalisar Yobe ya boye na mazabarsa

  • Hukumar ICPC da ke bincike kan ayyukan da gwamnati ta bayar a yi wa talakawa ta garkame wasu kadarori
  • An gano wani dakin ajiya dauke da masun keke-napep guda 29 da aka bayar a raba a jihar Yobe
  • Hakazalika, an gano wata cibiyar fasahar sadarwa daka aka gagara kammala ayyukanta a jihar

Yobe - Jami'an hukumar ICPC da ke bin diddigin aiwatar da ayyukan zartarwa da na mazabu sun garkame dakin adana kaya da wata cibiyar fasahar sadarwa (ICT) a karamar hukumar Potiskum ta jihar Yobe a ranar Alhamis 9 ga watan Satumba.

Dakin ajiyan, wanda ke unguwar Lailai, an yi amfani da shi ne don tara keke-napep 29 da aka bayar a raba a karkashin shirin Karfafawa Matasa (YES) ga gundumar Sanatan Yobe ta Kudu a 2020.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Hukumar ICPC ta kwato garkame kadarori da dan majalisar Yobe ya boye na mazabarsa
Jami'an ICPC: recruitmentgate.com
Asali: UGC

Ibrahim Bomai shine Sanatan dake wakiltar yankin a yanzu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ana zargin cibiyar ICT da ke kan titin Kano tana hannun wani dan majalisa da ya ki sakinta ga dan kwangila domin ya gyara ta kayayyakin aikin ICT.

Jami'an na ICPC sun yi nasarar duba ayyukan zartarwa da mazabu 52 a fadin jihar.

A daya daga cikin wuraren ayyukan, wani dan kwangila ya gaggauta zuwa don kammala kwangilar rijiyar burtsatse da aka bashi a shekarar 2019, lokacin da ya samu labarin zuwan jami'an bincike.

Jami'an ba su iya ziyartar ayyuka takwas ba saboda rashin tsaro da ambaliyar ruwa.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar ayyukan sun nuna godiya ga Gwamnatin Tarayya, inda suka ce ayyukan sun yi tasiri a rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina

Mukaddashin Daraktan Ayyuka na Jami'ar Tarayya da ke Gashua, Samuel Shula, ya ce rijiyar burtsatse da aka gina a cibiyar ta biya bukatun ruwa na jami'ar.

Ya lura cewa samar da rijiyar burtsatse da makamashin hasken rana maimakon man dizal, ya sa cibiyar ta sami saukin gudanar da ayyuka cikin sauki.

Mista Shula, ya yi tir da fashewar bututu da yawa da ke jikin rijiyar burtsatsen saboda dan kwangilar ya kasa binne su a cikin rami mai zurfin da ya kai milimita 900.

Abdurrassheed Bawa: Barayi suna amfani da Bitcoin wajen sace kudi a duniya

Abdulrasheed Bawa, shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ya ce kudaden intanet sun zama kyakkyawan zabi ga mutanen da ke gudanar da hada-hadar kudi ba bisa ka’ida ba, TheCable ta ruwaito.

Bawa ya fadi hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, a taron kasa da kasa na Cambridge karo na 38 kan laifukan tattalin arziki, mai taken, 'Laifin Tattalin Arziki: Wa Ya Biya kuma Wa Ya Kamata Ya Biya Farashi?'

Kara karanta wannan

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

Cibiyar Adana Bayanai ta Duniya kan Tsararrun Laifukan Tattalin Arziki (CIDOEC) a Kwalejin Jesus ta Jami'ar Cambridge a Burtaniya ce ta shirya taron.

CBN da wasu za su haɓaka tsarin gudanar da kasuwar Bitcoin

A wani labarin, Hukumar Tsaro da Musaya, babbar hukuma mai kula da kasuwar babban birnin kasar, ta ce za ta hada gwiwa da Babban Bankin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki don samar da tsari na yadda za a ke hada-hada da sauran kudaden intanet (Cryptocurrencies).

Darakta-Janar na SEC, Mista Lamido Yuguda, ya fadi haka a taron hadin gwiwa na kwamitin Majalisar Dattawa kan Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi, Manyan Kasuwanni da harkar fasahar sadarwa da Laifukan Intanet a Abuja, ranar Talata.

Babban Bankin na Najeriya a farkon wannan watan ya ba da umarni ga bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar da su rufe dukkan asusun kudaden intanet, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke dan bautar kasa da ke safarar alawa mai bugarwa daga UK

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel