Ba zama: 'Yan sanda sun ci alwashin kamo wadanda suka sace ma'aikatan Obasanjo

Ba zama: 'Yan sanda sun ci alwashin kamo wadanda suka sace ma'aikatan Obasanjo

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun ta tabbatar da sace wasu ma'iakatan kamfanin Obasanjo
  • A jiya ne wasu miyagun 'yan bindiga suka yi luguden wuta kan wata motar ma'aikatan kamfanin
  • Rundunar 'yan sandan ta ce lallai za ta ceto mutanen da aka sace, sannan zata kame 'yan bindigan

Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da sace ma’aikatan Obasanjo Holdings guda uku da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka sace su a kan babbar hanyar Kobape zuwa Abeokuta.

The Sun News ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ya bayar da tabbacin ne a Abeokuta, yayin tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an sace mutanen ne, a ranar Laraba, 8 ga Satumba, da misalin karfe 6 na yamma, a Kauyen Seseri, kusa da Kobape.

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Damke Kasurgumin Dan Bindiga da Wasu Yan Leken Asiri da Dama a Katsina

Rundunar ‘yan sandan ta ba da tabbacin cewa jami’an ta za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun ceto ma’aikatan.

Ba zama: 'Yan sanda sun ci alwashin kamo wadanda suka sace ma'aikatan Obasanjo
Rundunar 'yan sanda | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, ana kyautata zaton an shiga da ma’aikatan cikin daji, inda aka boye su a wani wurin da ba a sani ba.

Legit.ng ta tattaro cewa wadanda aka sace sun hada da mai kula da harkokin kudi, shugaban kididdiga na kudi da manajan ma'ajiyar kamfanin, wanda aka ce mallakar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne.

Yadda 'yan bindigan suka sace mutanen inji rahoton 'yan sanda

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigan sun yi musu kwanton bauna ne yayin da suke tuka mota kirar Toyota Hilux a kan wata babbar hanya.

Kakakin rundunar na Ogun yace:

“Sace mutanen ya faru ne da misalin karfe 6 na yamma a jiya. Obasanjo yana da gona kusa da yankin a Kobape.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace ma'aikatan Obasanjo 3 bayan yi wa motarsu luguden wuta

"Mutanen mu sun fara neman su kuma za mu tabbatar an kubutar da su."

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya nanata kudirin rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar, jaridar Nigerian Tribune ta kuma ruwaito.

Ya tabbatar wa mutanen jihar cewa nan ba da dadewa ba za a kamo masu garkuwa da mutanen, yayin da wadanda aka yi garkuwa da su din kuma za a ceto su.

'Yan bindiga sun sace ma'aikatan Obasanjo 3 bayan yi wa motarsu luguden wuta

A wani labarin, Miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikata 3 na tsohon shugaban kasa Olusegn Obasanjo a wani kauye da ke Abeokuta, jihar Ogun a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba.

The Punch ta ruwaito cewa, miyagun masu garkuwa da mutanen sun damke ma'aikatan kamfanin Obasanjo Holdinga da ke Kobape a karamar hukumar Obafemi-Owode da ke jihar.

Wata majiya da jaridar ta gani, ta ce ma'aikatan da aka sace sun hada da shugaban fannin kudi na kamfanin, shugaban bangaren kididdiga da kuma manajan wurin ajiye-ajiye.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun harbe 'yan sanda 3, sun kona gawarsu a Delta

Asali: Legit.ng

Online view pixel