Babban taro: Majiyoyin PDP sun ce tsofaffin gwamnoni na iya samar da shugaban jam’iyyar na kasa na gaba

Babban taro: Majiyoyin PDP sun ce tsofaffin gwamnoni na iya samar da shugaban jam’iyyar na kasa na gaba

  • Ga dukkan alamu rikicin da ke faruwa a jam'iyyar PDP na iya zuwa karshe nan ba da jimawa ba
  • A yanzu haka masu ruwa da tsaki na PDP suna shirya ma rayuwa bayan shugabancin babbar jam'iyyar adawa a kasar mai ci a yanzu
  • A yanzu haka tsofaffin gwamnoni a cikin jam’iyyar suna neman mukamai daban-daban wadanda za su kasance a babban taron PDP

FCT, Abuja - Wani rahoton jaridar Nigerian Tribune ya nuna cewa gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na iya ba tsoffin gwamnoni damar samar da shugaban jam’iyyar na kasa na gaba yayin da suka amince da yadda za a raba mukamai a Kwamitin Aiki na Kasa (NWC).

A ganawar da suka yi a Abuja a ranar Laraba, gwamnonin sun gayyaci sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a zaman don neman shigar da su cikin tsarin rabon mukaman na sabuwar kwamitin da za a zaba a babban taron kasa na Oktoba.

Kara karanta wannan

Sunday Igboho ya ce a mika shi ga Najeriya bai jin tsoron karo da gwamnatin Buhari

Babban taro: Majiyoyin PDP sun ce tsofaffin gwamnoni na iya samar da shugaban jam’iyyar na kasa na gaba
Babban taro: Majiyoyin PDP sun ce tsofaffin gwamnoni na iya samar da shugaban jam’iyyar na kasa na gaba Hoto: PDP
Asali: Facebook

An cimma matsaya kan a bai wa tsoffin gwamnoni da ministoci dama domin su fitar da 'yan takara.

Majiyoyi sun sanar da cewa bayan yarjejeniyar, tsoffin gwamnonin na iya samar da shugaban jam'iyyar na kasa na gaba don maye gurbin Prince Uche Secondus baya ga wasu yan tsirarun mukamai da aka ba su a yanzu.

Amma ba a bayyana ko taron ya amince da yankin kasar da sabon shugaban jam'iyyar zai fito ba.

Daga baya tsoffin masu rike da mukaman siyasa sun bar taron bayan kimanin sa’o’i biyar ana tattaunawa yayin da gwamnonin ke ci gaba da tattaunawa kan wasu batutuwa.

Daga cikin tsoffin gwamnonin da suka halarci taron akwai Ahmed Makarfi, Sule Lamido, Emeka Ihedioha, Babangida Aliyu, da Ibrahim Idris.

A halin da ake ciki, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar PDP sun taba ganawa da kungiyar tsoffin gwamnonin PDP, tsoffin ministoci, da tsoffin 'yan majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan bindiga sun gurzu, suna rokon jama'a yafiya tare da sako wadanda suka sace a Zamfara

Taron ya ta'allaka ne kan batun raba mukaman NWC gabanin babban zaben kasa na ranar 31 ga Oktoba.

Rigingimun PDP ya sa Gwamnonin Jam’iyyar adawa za su yi zama na 3 a cikin makonni 4

A wani labarin, gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP sun sa rana domin su zauna da nufin kawo karshen matsalolin da PDP ta ke ta fuskanta.

The Cable tace wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Darekta-Janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, C.I.D. Maduabum daga garin Abuja.

A jawabin da ya fitar jiya, Maduabum yace gwamnonin adawa za su yi taro a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba, 2021, domin shirya wa zaman NEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel