Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace ma'aikatan Obasanjo 3 bayan yi wa motarsu luguden wuta

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace ma'aikatan Obasanjo 3 bayan yi wa motarsu luguden wuta

  • 'Yan bindiga sun sace mutum 3 da ke aiki da kamfanin Obasanjo Holdings a Kobape a karamar hukumar Obafemi-Owode da ke jihar Ogun
  • Ma'aikatan tsohon shugaban kasan sun shiga hannun miyagun ne a yammacin ranar Laraba, 8 ga watan Satumba
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar mugun al'amarin

Obafemi-Owode, Ogun - Miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikata 3 na tsohon shugaban kasa Olusegn Obasanjo a wani kauye da ke Abeokuta, jihar Ogun a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba.

The Punch ta ruwaito cewa, miyagun masu garkuwa da mutanen sun damke ma'aikatan kamfanin Obasanjo Holdinga da ke Kobape a karamar hukumar Obafemi-Owode da ke jihar.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace ma'aikatan Obasanjo 3 bayan yi wa motarsu luguden wuta
Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace ma'aikatan Obasanjo 3 bayan yi wa motarsu luguden wuta. Hoto daga Xabiso Mkhabela/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Wata majiya da jaridar ta gani, ta ce ma'aikatan da aka sace sun hada da shugaban fannin kudi na kamfanin, shugaban bangaren kididdiga da kuma manajan wurin ajiye-ajiye.

Kara karanta wannan

An shiga halin fargaba yayin da cutar Kwalara ta kashe mutane 25 a Ogun

Majiyar ta ce:

"An sace su wurin karfe 4 na yammaci a kauyen Seseri bayan motarsu kirar Hilux ta sha ruwan wuta. A nan suka samu nasarar dauke su."

Kakakin ruundunar 'yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A cewarsa:

"Lamarin ya faru a ranar Laraba wurin karfe 4 na yammaci. Akwai gonar Obasanjo da ke kusa da yankin a Kobape."

'Yan bindiga sun shiga 3: NAF ta fara gwada sabbin jiragen Super Tucano

A wani labari na daban, yayin da jiragen yakin Najeriya ke cigaba da luguden wuta kan 'yan fashin daji a jihohin Zamfara da Kaduna, rundunar sojin sama ta Najeriya na gwada sabbin jiragen Super Tucano da Najeriya ta siya kwanan nan.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon sanata

PRNigeria ta ruwaito cewa, ministan tsaro, Janar Bashir Magashi mai ritaya ya bayyana hakan ga manema labarai bayan sa'o'i da suka kwashe suna taro kan tsaron kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda aka yi da hafsoshin tsaron kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ministan ya ce taron tsaron da suka yi da shugaban kasa ya sake duba halin tsaron kasar nan kuma sun yanke shawarar cewa, za a shawo kan matsalar tsaron, ballantana a jihar Zamfara da arewa ta tsakiya wanda ya zama gagarumin lamarin da suka tattauna a taron kuma ake neman hadin kan 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel