Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

  • Wasu jami'an 'yan sanda sun samu sabani tsakaninsu, lamarin da ya kai daya ya harbe daya
  • Rahoto ya bayyana cewa, jami'in ya harbe dan uwansa ne saboda yana masa dariya kawai
  • Tuni aka mika shi ga cibiyar bincike da CID don gudanar da bincike ciki har da lafiyar kwakwalwarsa

Kano - An harbe wani jami’in dan sanda mai suna Sufeto Ya’u Yakubu a hedkwatar ‘yan sanda na yankin Warawa da ke jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

An ce Sajan Basharu Alhassan ne, wani abokin aikinsa a sashen da suke ya harbe shi.

Yayin tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an garzaya da marigayin zuwa babban asibitin Wudil inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Kiyawa ya kara da cewa nan take aka cafke Sajan Basharu Alhassan.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin tsohon gwamnan Filato

Yanzu-Yanzu: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano
Jami'an 'yan sanda | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa yanzu haka an tura wanda ya yi kisan zuwa CID na jihar, za a yi masa gwaji don tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Dikko ya ba da umarni.

A cewar Kiyawa:

"An samu rashin fahimtar juna ne tsakanin jami'an biyu kuma a sakamakon haka, Sufeto ya harbi Sajan din."
“A bincikenmu na farko, sugeton ya ce bai ma san lokacin da ya harbe abokin aikin nasa ba kuma yana iya tuna cewa marigayin yana yi masa dariya. Don haka ya fita hayyacinsa kuma ya aikata wannan aikin."

Ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar ya ba da umurnin a mika karar zuwa sashen binciken manyan laifuka na CID na jihar, domin ba su damar gudanar da bincike na gaskiya a kan lamarin.

Kara karanta wannan

NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin tsohon gwamnan Filato

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wadanda suka kashe Pa Defwan Dariye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, inji rahoton jaridar Punch.

An kashe dattijon dan shekara 93 bayan da masu garkuwa da mutanen suka sace shi suka kuma karbi kudin fansa miliyan 10 daga iyalansa.

Jagoran gungun masu garkuwa da mutane, Jethro Nguyen, dan shekara 53, ya ce ya dauki hayar wasu mutane 10 ciki har da wasu Fulani makiyaya don sace tsohon a gidansa, ya kara da cewa sun tsare shi a maboyarsu na kusan kwanaki 10 kafin su hallaka shi.

Nguyen, wanda aka gabatar da shi a hedkwatar rundunar yan sanda a Abuja, ranar Laraba 8 ga watan Satumba, ya furta cewa ya ba daya daga cikin 'yan tawagarsa umarnin harbe tsohon.

Ya ce sun yi garkuwa da mamacin ne saboda za su iya samun kudi cikin sauki daga gareshi kasancewar dansa ya taba yin gwamna a jihar Filato, kuma sanata a Najeriya.

Kara karanta wannan

Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa

'Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

A wani labarin, 'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Kabir Muhammad Burkai, yaya ga Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.

Katsina Post ta ruwaito cewa yan bindigan sun saceshi ne ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a gonar sa dake wani kauye mai suna Daftau da rana, karamar hukumar DanMusa ta jihar.

Kabir Muhammad Burkai dai mahaifin su daya da Mustapha Inuwa sai dai ba mahaifiyar su daya ba. Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba’a samu labarin ko an sako shi ba kuma ‘yan bindigar ba su tuntubi yan uwansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel