Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun harbe 'yan sanda 3, sun kona gawarsu a Delta

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun harbe 'yan sanda 3, sun kona gawarsu a Delta

  • An shiga halin fargaba a garin Umutu, a ƙaramar hukumar Ukwuani ta jihar Delta, bayan kisan wasu jami'an 'yan sanda uku
  • Wasu 'yan bindiga ne suka far masu a wani shingen bincike sannan suka kona gawarsu bayan sun harbe su
  • Zuwa yanzu ba a ji ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar ba kan lamarin

Delta - Tashin hankali ya mamaye garin Umutu, a ƙaramar hukumar Ukwuani ta jihar Delta, bayan kisan wasu jami'an 'yan sanda uku na hedikwatar rundunar da ke garin.

Jaridar PM New ta ruwaito cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, ne suka kashe su da misalin karfe 7.40 na safiyar Laraba a wani shingen binciken ababen hawa da jami’an suka sanya a kan titin Obeti / Oliogo.

Kara karanta wannan

‘Yan banga 5 sun hadu da ajalinsu sakamakon harin ‘yan bindiga a hanyar Birnin Gwari

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun harbe 'yan sanda 3, sun kona gawarsu a Delta
'Yan bindiga sun harbe 'yan sanda 3, sun kona gawarsu a Delta Hoto: Crown fm
Asali: UGC

Majiyoyin yankin sun shaida wa jaridar cewa 'yan bindigar sun kuma kona motar sintiri kirar Toyota Sienna da aka ba sashen 'yan sanda na Umutu kwanan nan.

An kuma tattaro cewa yan bindigan sun bankawa mamatan wuta a cikin motar sintiri.

“An kai wa jami’an‘ yan sanda uku da ke aiki a hedikwatar rundunar ‘yan sanda na Umutu hari sannan aka kashe su a wurin binciken ababen hawa da ke tsakanin Obeti da Oliogo a karamar hukumar Ukwuani ta Delta.
"An kona su ta yadda ba za a iya gane su ba a cikin motocin sintiri na Toyota Sienna," in ji wata majiya a yankin.

Bayan faruwar lamarin, an ce tashin hankali ya mamaye mazauna Umutu, Obeti da Oliogo da sauran garuruwan da ke makwabtaka, saboda fargaban harin ramuwar gayya a kan al'ummomin ko kuma kamu daga hukumomin yan sanda.

Kara karanta wannan

An bindige hatsabiban 'yan fashi da suka kitsa kai hari ofishin 'yan sanda da kashe sifeta

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Hakanan, kokarin tabbatar da faruwar lamarin daga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), DSP Bright Edafe, ya ci tura.

A wani labarin, 'Yan bindigan da ake zargin sun tsere ne daga daga yankunan Bakura - Talata Mafara na jihar Zamfara, a ranar Talata, sun kai hari ƙaramar hukumar Dange Shuni a Sokoto sun sace a ƙalla mutum 20, Premium Times ta ruwaito.

A halin yanzu dai rundunar sojojin Nigeria da wasu hukumomin tsaro suna aikin ragargazar ƴan bindiga a dazukan Zamfara.

Saboda aikin da sojojin ke yi an datse hanyoyin sadarwa na salula da kuma kasuwannin sayar da dabbobi da dakatar da sayar da fetur a jarka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel