Hisbah Ta Kama Motoci Biyu Maƙare Da Katon Ɗin Giya 5,760 a Kano

Hisbah Ta Kama Motoci Biyu Maƙare Da Katon Ɗin Giya 5,760 a Kano

  • Hukumar Hisbah a jihar Kano ta yi nasarar kama motocci biyu dauke da katon din giya 5,760
  • Lawan Ibrahim Fagge, mai magana da yawun hukumar Hisbah ta Kano ne ya bayyana hakan
  • Sanarwar ta Fagge ta ce an kama motoccin ne yayin da jami'an hukumar ke bincike misalin karfe 4 na asuba a ranar Laraba

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama motoci biyu makare da katon 5,760 din giya daban-daban a kan hanyar Kano zuwa Madobi, rahoton News Wire NGR.

Hakan na cikin wata sanarwa ne da mai magana da yawun hukumar, Lawan Ibrahim Fagge ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Hisbah Ta Kama Motoci Biyu Maƙare Da Giya Daban-Daban a Kano
Hisbah Ta Kama Motoci Biyu Maƙare Da Giya Daban-Daban a Kano. Hoto: News Wire NGR
Asali: Facebook

Yadda aka kama giyan?

Sanarwar ta ruwaito cewa babban kwamandan Hisbah, Dr Harun Ibn Sina, yana cewa, a yayin da ake bincikar motoci a hedkwatar hukumar, ne jami'an Hisbah suka kama su misalin karfe na asubahin ranar Laraba.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke dan bautar kasa da ke safarar alawa mai bugarwa daga UK

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce,

"Hukumar ta Hisbah ta hana sayar da giya a jihar domin hana yin maye."

Ibn Sina ya kara da cewa hukumar za ta cigaba da yaki da miyagun kwayoyi da wasu ababen masu saka maye da matasa ke sha a jihar a cewar rahoton na News Wire NGR.

Ya yabawa kokarin jami'an na Hisbah, masu bada gudunmawa da masu ruwa da tsaki bisa jajircewarsu.

Ya kara da cewa halayen shaye-shaye tsakanin matasa a jihar ya zama babban abin damuwa ga al'umma baki daya.

Kazalika, Shugaban na Hisbah ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin kawar da kwayoyi da sauran kayan maye daga cikin al'umma.

Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

A wani labarin daban, Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani a su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.

Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel