Buhari a Imo: Inyamurai sun ce za su fito kwansu da kwarkwata su tarbi Buhari

Buhari a Imo: Inyamurai sun ce za su fito kwansu da kwarkwata su tarbi Buhari

  • Matasan kabilar Igbo sun ci alwashin taruwa don tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • A cewarsu, shugaban zai zo jihar Imo ne domin kaddamar da aikin da ya yi musu ba taron siyasa ba
  • Sun kuma gargadi masu kokarin ta da zaune a jihar da su kaucewa duk wani abin da zai kawo hargitsi

Imo - Matasan kabilar Igbo sun sha alwashin taruwa domin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Imo, a ranar Alhamis, lokacin da zai ziyarci jihar don kaddamar da ayyukan gwamnan jihar, Sanata Hope Uzodinma.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Onwuasoanya Jones Mataimakin Shugaban kungiyar matasan Igbo ta Ohanaeze Ndigbo Worldwide.

Buhari a Imo: Inyamurai sun ce za su fito kwansu da kwarkwata su tarbi Buhari
Taswirar jihar Imo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari, GCFR zai kasance a jihar Imo a ranar Alhamis 9 ga watan Satumba domin ziyarar aiki, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jajiberin zuwan Buhari Imo: Gwamnatin jiha ta ja kunnen 'yan IPOB da kakkausar murya

Ziyarar Shugaban a Imo ita ce ziyarar aiki ta farko a jihar tun hawan sa mulki a shekarar 2015 kuma a karon farko jihar za ta karbi bakuncin Shugaban kasa a ziyarar aiki tun 2009.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Onwuasoanya ya yi gargadin cewa duk wanda ke kokarin cin zarafin wadanda ke son zuwa don maraba da Shugaban kasar zuwa jihar Imo za a dauke shi a matsayin masu son tada zaune tsaye ba wai wanda ke wakiltar maslahar Igbo ba.

A cewarsa:

"Shugaban kasa ba zai zo ne don taron siyasa ba, sai dai don babbar harkallar da kowane dan jihar Imo na gaskiya ko dan Igbo ya kamata ya sa ido akai."

Gwamnatin jihar Imo na shirin tarbar shugaba Buhari, inji kwamishina

Kwamishinan yada labarai na Imo, Declan Emelumba, ya ce gwamnatin jihar na shirin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba a Owerri.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Imo na shirin tarbar shugaba Buhari, inji kwamishina

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa an shirya shugaban kasar zai kai ziyarar aiki zuwa Imo don kaddamar da wasu ayyukan da jihar ta aiwatar.

Emelumba ya ce shugaban zai kaddamar da muhimman ayyukan da Gwamna Hope Uzodimma ya fara a cikin watanni 18 da suka gabata.

A cewarsa:

“Mun shirya sosai don karbar bakuncin Shugaban kasa a Imo. An kammala duk wasu shirye-shirye.
"Da isowarsa, ana sa ran zai fara kaddamar da ayyuka, ciki har da hanyar Naze-Nekede-Ihiagwa-Obinze da titin karkashin kasa akan hanyar D-Tiger Owerri."

Ya ce Buhari zai kuma kaddamar da titin Egbeada da sabbin dakunan majalisar zartarwa na jihar a gidan gwamnati, da sauran su.

Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa

A wani labarin, sama da mambobin jam’iyyar APC 50,000 ciki har da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Mista Kobis Ari Themnu, sun koma PDP a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah za ta tura Fulani makiyaya Amurka domin a horar dasu kiwon zamani

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya tarbe su a dandalin Ribadu Square na taro a Yola ya zarge su da yin imani da kuma daidaita amincin su ga jam'iyyar da ta gaza tun farko, inji rahoton jdairdar Leadership.

Sai dai Atiku ya ce kuskuren su na kasancewa a cikin APC yanzu an gafarta musu, sannan ya kara tabbatar da cewa PDP ta shirya ta karbi mulkin kasar nan a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel