VAT: Shari’ar Gwamnatin Ribas da Gwamnatin Tarayya ya raba kan Jihohi zuwa gidaje 3

VAT: Shari’ar Gwamnatin Ribas da Gwamnatin Tarayya ya raba kan Jihohi zuwa gidaje 3

  • Shari’ar da ake yi tsakanin Gwamnatin Ribas da FIRS ta kawo sauyi a jihohi
  • Wasu Gwamnonin suna maraba da hukuncin kyale jihohi su tara VAT dinsu
  • Irin Adamawa suna tare da Ribas, Kogi ta fita dabam, wasu jihohi na tunani

A ranar Talata aka ji gwamnatocin Akwa Ibom da Adamawa suna tare da Mai girma gwamnan Ribas, Nyesom Wike kan batun karbar harajin VAT.

Darekta Janar na harkar yada labarai da sadarwa, Solomon Kumangar, ya yi hira da Punch, yace Adamawa na goyon bayan jihohi su rika karbar haraji.

Solomon Kumangar yake cewa hakan zai sa gwamnatocin jihohi su rage dogara da gwamnatin tarayya.

Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom, ta bayyana cewa za ta fara aiki domin a kawo kudirin da zai ba gwamnatin jiha damar tattara VAT a Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Sunday Igboho ya ce a mika shi ga Najeriya bai jin tsoron karo da gwamnatin Buhari

Honarabul Aniefiok Akpan wanda shi ne shugaban kwamitin yada labarai a majalisar dokokin Akwa Ibom, yace kwanan nan za ayi a doka a majalisa.

Legas tana tare da A/Ibom, Ribas

Rahoton yana cewa haka abin yake a Legas inda kudirin VAT ya tsallake mataki na biyu a majalisar dokoki, ana sa ran ya zama doka ba da dadewa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnati na zama
Buhari yana taro da Gwamnoni Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Gwamnonin Ekiti, Osun da Benuwai ba su tsaida magana ba, sun bayyana cewa sai sun fahimci yadda lamarin yake kafin su san matakin da za a dauka.

Bayelsa, Osun, Ekiti da Benuwai suna kan katanga

Akintunde Oyebode yace sai sun saurari ra’ayin masana shari’a sannan za su san abin yi a Ekiti. Wannan shi ne ra’ayin takwarorinsa a Benuwai da Osun.

Shi ma Kwamishinan labarai na Bayelsa, Ayibaina Duba yace sun zakulo masana da nufin bibiyar shari’ar da ake yi a kotu domin sanin ina mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina

Kwamishinan Kogi, Ashiru Idris yace ba su la’akari da karbar VAT, yace wannan bai gaban gwamnatinsu domin ba zai iya kara masu kudin-shiga ba.

Gombe tana lallabar jihohin Kudu

Daily Trust tace jihar Gombe ba ta ganin kyale jihohi su karbi harajin VAT ba shi ne mafita, tace zai fi kyau a bar gwamnatin tarayya da wannan dawainiya.

A wajen wani taron kara wa juna sani, Kwamishinan kudi na Gombe, Muhammad Magaji ya roki jihohi kudu su cire son rai, su bari a rika raba kason a tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel