Malamin addini ya bayyana illar zaɓar miji saboda kyawun sa ba tare da neman zaɓin Ubangiji ba

Malamin addini ya bayyana illar zaɓar miji saboda kyawun sa ba tare da neman zaɓin Ubangiji ba

  • Ko wacce mace ta na da irin abubuwan da ta ke gani dangane da namijin da za ta so ta aura
  • Wasu sun fi zaben kyau, wasu kuma dukiya, nagarta ko kuma wata manufa ta daban
  • Fasto Leke Adeboye ya shawarci mata da su mika zabin su ga Ubangiji su daina kallon kyau

A zamanin nan, mata da dama suna da dalili na soyayya ko kuma zaben mijin da suke so su aura, shafin LIB ya ruwaito.

Wasu matan sun gwammaci su zabi farin namiji, wasu kuma baki. Wasu gajere ko kuma dogo. Yayin da wasu ba su kallon ko wanne daga cikin wadannan, sun gwammaci mai tarin dukiya.

Fasto ya bayyana illar zaɓar miji saboda kyawun sa ba tare da neman zaɓin Ubangiji ba
Fasto ya bukaci mata da su daina aure kyau ba tare da neman zabin ubangiji ba. Hoto daga Leke Adeboye
Asali: Facebook

Wani fasto mai suna Leke Adeboye ya bai wa mata shawara a kan zabin namijin da za su aura inda ya ce kada su kalli wata surar sa

Kara karanta wannan

Yadda matashi a Gombe ya dale karfen sabis ya ce ba zai sauko ba sai an masa aure

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar faston, ya kamata su bai wa Ubangiji zabi don hakan shi ne mafi dacewa. Ya bayar da wadannan shawarwarin ne ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

Kamar yadda ya wallafa:

“Ya kamata mata su nemi zabin Ubangiji wurin zaben abokin rayuwa ba wata surar sa ba.”

An bindige hatsabiban 'yan fashi da suka kitsa kai hari ofishin 'yan sanda da kashe sifeta

A wani labari na daban, 'yan sanda a Imo sun ce sun bindige wasu hatsabiban 'yan fashi da makami biyu, wadanda su da tawagarsu suka dade suna addabar mutanen garin Obiakpo a karamar hukumar Ohaji na jihar, rahoton Daily Trust.

Sanawar da kakakin yan sandan jihar CSP Mike Abattam ya fitar ta ce yan sandan bayan samun bayannan sirri sun kai samame mabuyar shugaban tawagar suka kashe shugaban, Modestus Ugwuoha wanda aka fi sani da 'Modukpe' da wani guda.

Kara karanta wannan

Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo

Ya ce sauran 'yan tawagar sun tsere da raunin bindiga a jikinsu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ya kara da cewa jami'an yan sandan suna bin sahun sauran yan tawagar da suka tsere. A cewar Abattam, tawagar ce ta kitsa harin da aka kai ofishin yan sanda na Njaba tare da kashe jami'i mai mukamin sufeta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel