'Yan bindigan Zamfara 'yan ta'adda ne ba 'yan fashi ba, Cewar Akeredolu

'Yan bindigan Zamfara 'yan ta'adda ne ba 'yan fashi ba, Cewar Akeredolu

  • Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana 'yan bindigar da ke kai farmaki kan garuruwa daban-daban a jihar Zamfara a matsayin' yan ta'adda
  • A cewar gwamnan na jihar Ondo, 'yan bindigar ba 'yan fashi ba ne kamar yadda ake kiran su, sai dai 'yan ta'adda
  • Gwamnan ya yi wannan tsokaci ne yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Jami'ar Fasaha ta Tarayya, Akure

Akure - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya ce 'yan bindigar da ake kira 'yan fashi a Zamfara 'yan ta'adda ne, jaridar Punch ta ruwaito.

Akeredolu ya fadi hakan ne a ranar Talata, 7 ga watan Satumba yayin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gudanarwa na Jami'ar Fasaha ta Tarayya, Akure.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

'Yan bindigan Zamfara 'yan ta'adda ne ba 'yan fashi ba, Cewar Akeredolu
Rotomi Akeredolu ya ce 'yan bindigan Zamfara 'yan ta'adda ne ba 'yan fashi ba Hoto: Ondo state government
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Legit.ng ta gani kuma kakakin gwamnan, Richard Olatunde ya saki.

An nakalto Akeredolu yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Dubi abin da ke faruwa a Zamfara. Suna ƙoƙarin suturta shi sannan kuma suna kiransu 'yan fashi. 'Yan ta'adda ne. Don haka, ci gaban kimiyya ba zai dogara ne akan cajin ku kawai ba illa a kan yanayin da ya dace a ƙasar.”

'Yan ta'adda ba 'yan fashi ba ne'

Hakazalika, Abubakar Bagudu, gwamnan jihar Kebbi ya nuna damuwa kan ayyukan ‘yan fashi da ke haddasa barna a fadin kasar.

Bagudu a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba ya nemi gwamnatin da Buhari ke jagoranta ta ayyana barayin a matsayin 'yan ta'adda.

Magashi: 'Yan fashin daji sun zama fitina, 'yan Najeriya ba su yarda za mu iya maganinsu ba

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnonin APC 5 da ka iya tsayawa takara a gefen Goodluck Jonathan

A wani labarin, Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce 'yan bindiga suna tada hankula a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

TheCable ta ruwaito cewa, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bukatar a gaggauta magance matsalar su.

Ministan ya sanar da hakan a ranar Talata bayan taron majalisar tsaro da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Villa, Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel