Zargin SSS da kutse: Kotu ta yarda da bidiyoyin da aka mika gaban ta a shaidar gidan Igboho

Zargin SSS da kutse: Kotu ta yarda da bidiyoyin da aka mika gaban ta a shaidar gidan Igboho

  • Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Ibadan ta aminta da bidiyoyin da lauyan Igboho ya mika na kutsen DSS a gidansa
  • Har ila yau, kotun ta amince da cewa bidiyon da DSS ta mika ta lalata shi, lamarin da yasa ta fara kare kan ta
  • Sai dai kuma lauyoyin Malami da na DSS sun ce ya zama dole a je a gwada jinin da aka gani a bidiyon don tabbatar da cewa na mutum ne ko dabba

Ibadan - Wata babbar kotun da ke zama a Ibadan a ranar Talata ta yarda da bidiyoyin shaida da aka mika gaban ta kan zargin kutsen da jami'an tsaron farin kaya suka yi a gidan Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho a ranar 1 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke dan bautar kasa da ke safarar alawa mai bugarwa daga UK

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa, lauyan Igboho, Yomi Aliyu, SAN, ya mika kara tare da bukatar a biya shi diyyar biliyan N500 daga wurin antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, SSS da kuma daraktan DSS na jihar Oyo a kan kutse.

Zargin SSS da kutse: Kotu ta yarda da bidiyoyin da aka mika gaban ta a shaidar gidan Igboho
Kotu ta yarda da bidiyoyin da aka mika gaban ta a shaidar gidan Igboho. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Tun farko Aliyu ya sanar da kotun cewa, an kutsa gidan wanda ya ke karewa da motocinsa kuma an ragargaza tare da kashe wasu mutum biyu.

A zaman ranar Talata, Mai shari'a Ladiran Akintola, ya yarda da shaidun da aka mika gabansa bayan Aliyu ya bayyana asalin dalilin da yasa suka gurfana a gaban kotu, Daily Nigerian ta wallafa.

Akintola ya sake yadda da bidiyon da lauyan DSS ya mika, T. A. Nurudeen, inda Igboho ke barazanar kafar jamhuriyar Oduduwa, balle wa daga Najeriya da kuma kiran Yarabawa da su kare kan su da layu da bindigogi.

Kara karanta wannan

Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani

Kotun ta bukaci a saka bidiyoyin biyu a bayyane a kotu kamar yadda lauyan Igboho da na SSS suka bukata.

A yayin jawabi ga kotun bayan an saka bidiyoyin, lauyan AGF, Abdullah Abubakar, ya ce ba bu shaida a gaban kotu kan cewa jinin da aka gani a bidiyon ko na mutum ne.

Abubakar ya kara da cewa, babu wani abu a bidiyon da ya nuna cewa gidan da aka kutsa na Igboho ne ko kuma kutsen ya na da alaka da AGF.

Don haka ya yi kira ga kotun da ta yi watsi da duk wata shaida tare da korar karar da aka shigar.

Lauyan SSS, Nurudeen, ya ce tabbas ya zama wajibi likitoci masana halittar jini su tabbatar da cewa wannan jinin na mutum ne ba na mage ba.

Akintola ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba domin yanke hukunci.

Daga Zamfara zuwa Kaduna: Jirgin yakin NAF ya kone sansanin 'yan bindiga, an kashe 50 a dajin Kawara

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

A wani labari na daban, a sakamakon tashi tsaye da gwamnati ta yi wurin kawo karshen ta'addanci a wasu jihohin arewa, dakarun soji suna ta kai da kawowa tsakanin Zamfara zuwa wasu jihohi a cikin kwanakin nan.

Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar kone wani sansanin 'yan fashin daji da ke jihar Kaduna.

Kamar yadda PRNigeria ta tattaro, miyagun suna amfani da sansanin wurin buya a dajin Kawara da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel