Buhari Ya Gode Mana Bisa Kokarin da Muke Yi, IGP Ya Magantu Bayan Taron Tsaro a Aso Villa

Buhari Ya Gode Mana Bisa Kokarin da Muke Yi, IGP Ya Magantu Bayan Taron Tsaro a Aso Villa

  • Sufeta Janar na rundunar yan sandan Ƙasar nan, Usman Baba, yace Buhari ya yabawa shugabannin tsaro bisa kokarin da suke yi
  • IGP ya bayyana cewa shugaban ya umarci a ƙara zage dantse domin kawo karshen kalubalen tsaron da ya addabi ƙasa
  • A cewar sufeta janar shugabannin tsaron sun ɗaukarwa Buhari alkawarin ninka kokarin su fiye da baya

Abuja - Shugaba Buhari ya yabawa shugabannin tsaro a wurin taronsu na yau amma ya umarce su da su ƙara zage dantse domin kawo karshe matsalar tsaro baki ɗaya.

Sufeto Janar na rundunar yan sandan ƙasar nan, Usman Baba, Shine ya faɗi haka bayan ya halarci taron tsaro da ya gudanar a fadar shugaban ƙasa, Abuja, ranar Talata.

Dailytrust ta ruwaito cewa Shugaba Buhari ya karɓi bayanai daga bakin shugabannin tsaro kan halin da ƙasa take ciki.

Kara karanta wannan

Ku Gaggauta Nemo Dabarun Magance Matsalar Tsaron Najeriya, Buhari Ya Umarci Hafsoshin Tsaro

Da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati, Usman Baba, yace Buhari ya umarci su ninka kokarin da suke domin kawo karshen kalubalen tsaron da ya addabi Najeriya.

Shugaba Buhari tare da IGP
Buhari Ya Gode Mana Bisa Kokarin da Muke Yi, IGP Ya Magantu Bayan Taron Tsaro a Aso Villa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar shugaba Buhari sai an samu ingantaccen tsaro sannan yan Najeriya zasu samu damar cigaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba, kamar yadda channels tv ta ruwaito

Wane umarni Buhari ya sake baiwa shugabannin tsaro?

Sufeta Janar yace:

"Mun tattauna a wurin taron tsaro, hafsoshin tsaro da shugabannin ɓangaren fasaha sun yiwa Buhari bayani kan halin tsaron da ake ciki a ƙasa."
"Shugaban ƙasa ya yi nazari sannan ya yi jawabin cewa doka ta ɗorawa gwamnati alhakin samar da tsaro ga yan ƙasa, kuma a shirye yake ya yi duk abinda ya dace."
"Ya umarci mu kara zage dantse a kokarin da muke domin yana haifar da ɗa mai ido a arewa-gabas, kudu-gabas amma da sauran aiki a arewa ta tsakiya da arewa ta yamma, inda mutane suke kokawa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Tsaro a Fadarsa Aso Villa

Mun ɗaukar wa Buhari Alkawari- IGP

Sufetan yan sandan ya bayyana cewa shugabannin tsaro sun tabbatarwa Buhari cewa zasu ninka kokarin da suke yi domin baiwa mara ɗa kunya.

"Buhari ya gode mana kuma ya yaba mana kan kokarin da muka yi zuwa yanzun, sai dai ya bukaci mu kara akan da domin mutane su samu damar fita kasuwancin su yadda ya kamata."

A wani labarin kuma An Shiga Tashin Hankali a Wata Jami'a Yayin da Malamai Uku Suka Mutu Rana Daya

An shiga yanayin ruɗani da jimami a jami'ar jihar Abia yayin da malaman makarantar uku suka kwanta dama a rana ɗaya.

Rahotanni sun bayyana cewa har yanzun ba'a gano musabbabin mutuwar malaman uku ba, cikinsu harda Farfesa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel