Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari

Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta kai ziyara jihar Filato don tattauna batun kashe-kashen da suke faruwa a jihar
  • Shugaba Buhari ya ce sam gwamnatinsa ba za ta tsaya ba har sai ta tabbatar da hukunta masu kashe mutane a jihar
  • Ya kuma ce, gwamnati za ta zakulo masu karya doka da oda sannan ta gurfanar dasu a gaban kuliya

Plateau - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar cafke mutanen da ke da hannu a kashe-kashen da aka yi a jihar Filato, inji rahoton TheCable.

A cikin watanni uku da suka gabata, hare-hare a sassa daban-daban na jihar sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari.

Buhari, wanda Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya wakilta, a wani zaman tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki a jihar a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, ya bukaci tattaunawa mai dorewa don samar da zaman lafiya a Filato.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtinesng.com
Asali: UGC

Ya nemi hadin kan shugabannin gargajiya, na addini da na al'umma don inganta zaman lafiya a jihar, sannan ya kuma yabawa Simon Lalong, gwamnan jihar ta Filato, kan kafa majalisar addinai don dakile matsaloli.

Shugaban ya ce makasudin taron shi ne gina tubalin tattaunawa don saukake fahimta tsakanin kabilu, adalci, da karfafa amincewar mutane.

A cewarsa, dabarun samar da zaman lafiya a jihar “dole ne ya kasance mai girma, fadi, gaskiya da dorewa".

Buhari ya kuma ba da tabbacin cewa "gwamnati ta dage kan ci gaba da kare dukkan 'yan kasa masu son zaman lafiya, masu bin doka da al'ummominsu".

Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar Filato cewa:

“Gwamnati ta kuduri aniyar ci gaba da inganta zaman lafiya, hakuri da addinan juna ta hanyar tattaunawa da shiga tsakani”.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba

Shugaban ya tabbatar wa mazauna jihar Filato cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa, ya kara da cewa an tura karin jami’an tsaro jihar.

Ya kuma jajantawa gwamna Lalong da mutanen jihar Filato kan kashe-kashen da aka yi kwanan nan, inda ya kwatanta hare-haren a matsayin tsagwaran "rashin imani".

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an hukunta duk mutanen da aka samu da hannu dangane da hare-haren da aka kai kwanan nan a jihar Filato, The Cable ta ruwaito.

An kai hare-hare kan mutane da dama a garin Jos, babban birnin jihar Filato, da sauran sassan kasar a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda ya yi sanadiyar kashe-kashen mutane da dama, yayin da wasu mazauna garin da dama suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Sakamakon hare-haren da aka kai a Jos wasu gwamnatocin jihohi sun kwashe 'yan asalin jihohinsu dake karatu daga jihar ta Filato.

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

A wani labarin, Sama da dalibai 70 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata, PR Nigeria ta ruwaito.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari. An tsare daliban Islamiyyar na tsawon kwanaki 88 da awanni 11 gwargwadon lokacin da suka shafe a hannun 'yan bindigan kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel