Bayan Datse Sabis a Zamfara, Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Datse Sabis a Jihar Katsina

Bayan Datse Sabis a Zamfara, Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Datse Sabis a Jihar Katsina

  • Gwamnatin tarayya ta musanta jita-jitar cewa ta bada umarnin a katse sabis din layukan sadarwa a jihar Katsina
  • Shugaban hukumar sadarwa ta ƙasa NCC, Farfesa Danbatta, yace labarin ba shi da tushe ballantana makama
  • Ya umarci ɗaukacin al'ummar jihar Katsina da su yi watsi da rahoton domin ba daga NCC ya fito ba

Abuja - Hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta musanta raɗe-raɗin dake yawo a kafafen sada zumunta cewa ta baiwa kamfanonin sadarwa umarnin ɗauke sabis a jihar Katsina, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kakakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Abdu Labaran, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Litinin a Katsina.

Yace shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar Ɗanbatta, wanda ya yi magana da gwamnatin Katsina, yace rahoton ƙarya ne.

Kara karanta wannan

Ba Inda Zanje, Nima Zan Ɗanɗani Duk Wahalar da Jama'ata Ke Ciki, Matawalle Ya Soke Duk Wani Fita Zamfara

Babu shirin datse sabis a Katsina
Bayan Datse Sabis a Zamfara, Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Datse Sabis a Jihar Katsina Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sanarwar tace:

"Shugaban NCC, Farfesa Danbatta yace takardar da ake yaɗawa a ƙafafem sada zumunta kwafin wadda aka tura Zamfara ce."

A cewar kakakin gwamna Masari, Ɗanbatta ya bukaci a yi watsi da duk wata jita-jita da ake yaɗawa kan wannan domin sam ba daga hukumar ya hito ba.

Meyasa aka rufe sabis din sadarwa a Zamfara?

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa a kwanan nan hukumar NCC ta aike da takardar dake kunshe da umarni ga kamfanonin sadarwa su katse sabis ɗin sadarwa a jihar Zamfara.

Hukumar ta ɗauki wannan matakin ne domin taimakawa wajen dakile matsalar tsaron dake kara ruruwa a jihar.

Hakazalika, gwamnan jihar ta Zamfara, Bello Matawalle, ya bada umarnin kulle wasu kasuwanni da tashoshin mota, sannan kuma ya hana siyar da man fetur a kan hanya.

Kara karanta wannan

Zaben Kananan Hukumomi: Yan Daba Sun Sace Na'urar Zaɓe Sama da 40 a Kaduna, El-Rufa'i Ya Magantu

Matakan sun fara haifar da ɗa mai ido

A wata hira da ya yi a gida Rediyon DW, Gwamna Matawalle, yace matakan da gwamnatinsa ta ɗauka ya fara haifar da ɗa mai ido, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Bugu da ƙari yace yan bindiga sun fara sako mutanen da suka kama don tilas domin ba su da abincin da zasu cigaba da ba su.

A wani labarin kuma Ɓarayi Sun Sace Dalibai 1,409 a Najeriya Cikin Watanni 19, Miliyoyi Sun Salwanta Wajen Fansa

Wani sabon rahoto da ƙungiyar fasaha ta SBM ta fitar ya nuna cewa aƙalla ɗalibai 1,409 aka sace a faɗin Najeriya cikin watanni 19 da suka shuɗe.

Rahoton wanda akai wa take, "Sace ɗalibai daga makarantu a Najeriya," kungiyar ta bayyana adadin waɗanda hare-haren suka shafa tun daga watan Maris, 2020, zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel