Tirkashi: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon sanata

Tirkashi: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon sanata

  • 'Yan bindiga sun sace tsohon Sanatan da ya wakilci Kudancin Akwa Ibom a Majalisar Dattijai ta takwas, Sanata Nelson Effiong
  • Maharan sun yi awon gaba da dan siyasar wanda kuma tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ne daga wani masauki da ke kan titin Oron na birnin Uyo da daren Lahadi
  • Sun kuma jikkata wasu mutum takwas a yayin yunkurin sace tsohon Sanatan

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa akalla mutane takwas ne suka jikkata a wani turmutsitsin yayin da wasu yan bindiga suka yi awon gaba da Sanata Nelson Effiong, tsohon sanatan da ke wakiltar Akwa Ibom ta Kudu a majalisar dattawa.

An tattaro cewa wasu 'yan daba uku dauke da makamai sun yi ram da Sanatan a masaukinsa, da ke hanyar Oron, Uyo, babbar birnin jihar a daren ranar Lahadi, 5 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

Tirkashi: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon sanata
'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon sanata Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An samu rahoton cewa takwas daga cikin kwastomomin sun ji rauni a sakamakon turmutsitsi yayin da mutanen suka yi ta tserewa domin tsira da rayukansu a lokacin da 'yan bindigar suke ta harbi ba kakkautawa.

“An harbe ni a kan hanyar Oron,” Erick Ekwere, daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su ya koka a shafukan sada zumunta, inda ya bukaci hukumomin tsaro da su kawo agaji a lamarin.

“Lamarin ya faru da misalin karfe 9:00 na daren Lahadi. 'Yan bindigar sun kutsa cikin masaukin da motar Toyota Camry inda suka fara harbi ba kakkautawa, inda suka jefa abokan huldar da sauran baki cikin rudani da gudu don tsira kafin su tafi kai tsaye ga tsohon Sanatan, ”inji wata majiya.

Majiyar ta kara da cewa daga baya 'yan daba sun dauke Effiong a cikin mota Toyota Camry zuwa inda ba a sani ba don neman kudin fansa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Odiko Macdon ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce suna nan suna bincike a kai, Aminiya ta ruwaito.

Ya ce:

“Na yi imanin nan ba da jimawa ba, za mu ceto shi. Kwamishinan ’yan sanda ya kuma yi Allah-wadai da harin kuma ba za a yi wata-wata ba wajen ceto shi."

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin Shugaban karamar hukuma a jihar Bayelsa

A wani lamarin, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a daren ranar Lahadi sun sace Cif Gbalipre Turner, mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa, Hon. Ebinyo Marvin Turner.

An sace Cif Turner, wanda ya kuma kasance mamba mai ci a hukumar tara kudaden shiga ta jihar Bayelsa daga gidansa da ke kan hanyar Samphino a Yenagoa, babban birnin jihar.

Wata majiya daga iyalan ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa wasu ‘yan bindiga masu dauke da makamai na AK47 ne suka sace Turner, wanda shekarunsa ba su wuce 70 ba, da misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi sannan suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Mutum uku sun mutu yayin da miyagun Yan bindiga suka kai sabon hari jihar Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel