Tsohon ministan yada labarai a lokacin mulkin Janar Babangida ya rasu

Tsohon ministan yada labarai a lokacin mulkin Janar Babangida ya rasu

  • Tsohon shugaban mulkin soja na jihar Ribas ya riga mu gidan gaskiya bayan wata jinya da ya yi
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, tsohon shugaban ya kasance tsohon minista a zamanin Janar Babangida
  • Ya rasu ne da safiyar yau Litinin 6 ga watan Satumba kamar yadda rahoto ya bayyana

Ribas - Tsohon Ministan Yada Labarai a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida kuma daga baya ya zama Shugaban Soja na Jihar Ribas, Birgediya Janar Anthony Ukpo mai ritaya ya rasu.

Birgediya Janar Anthony Ukpo ya rasu da safiyar Litinin 6 ga watan Satumba, Daily Trust ta ruwaito.

Lauyan tsarin mulki, Leonard Anyogu, sakataren kwamitin kirkirar jihar Ogoja wanda Ukpo ke jagoranta, ya tabbatar da mutuwar tsohon shugaban sojin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya aurar da diyarsa Hauwa ga dan Sarkin Azara

A makon da ya gabata, biyu daga cikin manyan 'yan uwansa sun mutu.

Da Dumi-Dumi: Tsohon minista a lokacin mulkin Janar Babangida ya rasu
Taswirar jihar Ribas | Hoto: naijanews.com
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rasu jim kadan bayan mutuwar 'yan uwansa

Madam Lydia Ukpo ta mutu a Amurka, yayin da Archbishop Joseph Edra Ukpo shima ya mutu.

Anyogu ya bayyana cewa Ukpo ya mutu da sanyin safiyar Litinin a wani asibiti.

Ya ce Ukpo ya mutu sakamakon ciwon da ya dade yana fama dashi.

Ya ce:

“Zan iya tabbatar da cewa tsohon shugaban sojin ya mutu da safiyar yau. Ya rasu a asibiti a safiyar yau.

A cewar rahoton AIT, marigayin ya rasu yana shekaru 74 a duniya, kuma ya yi gwagwarmaya da hidima ga kasa.

Doka a Zamfara: Gwamna ya ba da umarnin a harbe masu goyon biyu a babur

Kamar dai a jihar ta Kaduna, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da umarnin rufe dukkan kasuwannin mako-mako a jihar a matsayin wani mataki na magance matsalar tabarbarewar tsaro a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Wasu manyan jiga-jigan PDP 3 sun sake sauya sheka zuwa APC

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa gwamna Matawalle ya sanar da hakan ne bayan ya karbi dalibai 18 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Aikin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar dake garin Bakura.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar ta hana sayar da man fetur a cikin jarkoki a wani mataki na dakile samar da man ga 'yan bindiga, hakazalika da kuma ba da umarnin harbin masu daukar biyu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel