FG za ta karbo miliyoyin naira da ta tura wa likitoci 588 bisa kuskure

FG za ta karbo miliyoyin naira da ta tura wa likitoci 588 bisa kuskure

  • Gwamnatin tarayya za ta karbo miliyoyin nairorin da ta yi kuskuren biyan likitoci 588 da ke fadin kasar nan
  • Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ne bayyana hakan yayin amsa tambayoyin maneman labaran gidan gwamnati a Abuja
  • Ya bayyana cewa an biya likitocin bisa kuskure ne maimakon wasu bangaren likitocin na daban yanzu haka wasunsu sun fara mayar da kudaden

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya za ta amso miliyoyin nairorin da ta biya likitoci 588 da ke fadin kasar nan bisa kuskure.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan kwadago da ayyuka, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran gidan gwamnati a Abuja.

Ya bayyana yadda kudaden suka shiga asusan likitoci na daban maimakon na likitoci masu neman kwarewa.

FG za ta karbo miliyoyin naira da ta tura wa likitoci 588 bisa kuskure
FG za ta karbo miliyoyin naira da ta tura wa likitoci 588 bisa kuskure. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar sa, bayan shugabannin likitocin asibitocin Najeriya sun zauna sun bi daki-daki ne suka tattaro sunaye 8000 na likitocin, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan ya bayyana yadda wasu daga cikin likitocin suka fara maido da kudaden yayin da ake kokarin ganin an tattaro sauran kudaden.

Ya bayyana yadda rashin karashe biyan kudade yake kara janyo gwamnati ta na daukar lokaci wurin biyan likitoci masu neman kwarewa.

“Mun yi bincike karo na farko kuma yanzu haka makarantun horar da likitoci sun bayyana sunayen su, masu neman kwarewa. An tattaro sunayen wurin 8000 kuma yanzu haka ma’aikatar lafiya ta na karasa bincike a kan su.
“Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kowanne makarantar likitoci ta na aiki da shugaban likitocin wurin ganin sun tattara duk sunayen su.
“Wannan dalilin ne ya janyo bacin lokaci wurin biyan likitoci masu neman kwarewa kudaden su wanda ya kamata ma’aikatar kudi ta ke kokarin yi,” a cewarsa.
"Sannan ya kara da bayyana yadda gwamnati za ta bi dokar ‘babu aiki babu biya’ saboda kusan ko wacce kasa ta na aiwatar da hakan, yadda ya auku a 2020. A 2020, ba a binciki sunayen da aka kawo ba ne da kyau.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti, sun kai wa likitoci da marasa lafiya farmaki

Sannan ya kara da bayyana yadda gwamnati za ta bi dokar ‘babu aiki babu biya’ saboda kusan ko wacce kasa ta na aiwatar da hakan.

Kano: Dan kwangila ya kai shugaban karamar hukuma kara wurin EFCC kan rike mishi N14.9m

A wani labari na daban, wani dan kwangila, Mustapha Umar-Tallo ya mika takardu 2 zuwa ofishin hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ya na zargin shugaban karamar hukumar Gwarzo, Bashir Abdullahi da kin biyan shi kudaden kwangilar da yayi na karamar hukumar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Umar-Tallo, ya rubuta takardar ta lauyan sa, Abubakar Lagazab, inda ya ke zargin shugaban karamar hukumar da kin biyan su kudaden duk da gwamnatin jihar ta riga ta biya kudaden.

A takardar ta ranar 17 ga watan Nuwamba 2020 wacce ya bayyana ta ga manema labaran jihar Kano a ranar Alhamis, Umar-Tallo ya zargi shugaban karamar hukumar da lamushe kudaden ayyuka 20 na kwadago da ayyuka 14 na karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

Asali: Legit.ng

Online view pixel