Rashin tsaro: ‘Yan bindiga sun hallaka Mai sarauta, sun dauke mutane a jihar Shugaban kasa

Rashin tsaro: ‘Yan bindiga sun hallaka Mai sarauta, sun dauke mutane a jihar Shugaban kasa

‘Yan bindiga sun hallaka Mai Unguwar Masaku da ke karkashin Kankara

Ana zargin ‘yan bindiga sun kashe Basaraken ne a daren Asabar a Katsina

Rahotanni sun ce an dauke ‘yan mata da dabbobi a wasu garuruwan jihar

Katsina - A ranar Asabar, 4 ga watan Satumba, 2021, aka ji wasu ‘yan bindiga sun auka wa kauyen Masaku da ke Gundawa a karamar hukumar Kankara.

Labarin da ya fito daga Katsina Post ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi nasarar kashe Mai unguwar garin Masaku da ke jihar Katsina a wannan hari.

Jaridar ta bada sunan wannan basarake da aka kashe a karamar hukumar Kankara da Malam Yahuza.

An yi ta'adi a kauyukan Katsina

Bayan kisan da suka yi, wadannan mutane da ba a san su wanene ba, sun yi gaba da dabbobi rututu daga karkarar, daga ciki akwai tumaki da kuma shanu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 22 don an kashe musu 'yan uwa a Neja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun ba yau ba ana fama da matsalar rashin tsaro a garin Kankara da kauyukan da ke kewaye. Garin Gundawa yana cikin wuraren ‘yan bindiga suka addaba.

A daidai wannan lokaci, rahoton ya kara da cewa ‘yan bindigan sun shiga garin Bakam a karkashin karamar hukumar Musawa a Katsina, sun yi barna.

Buhari da Aminu Bello Masari
Buhari da Aminu Bello Masari a Katsina Hoto: www.mutiuokediran.com
Asali: UGC

Lamarin rashin tsaro a Katsina bai tsaya a nan ba, ‘yan bindigan sun shiga kauyen Hayin Gidan Tambai, kuma har sun yi nasarar dauke wasu mutane biyu.

A garin Damawa, miyagun sun yi awon-gaba da ‘yan mata biyu da ake tunani za su nemi a biya su kudin fansarsu. Sannan sun saci awakin mutanen garin.

Wadannan hare-hare suna zuwa ne a daidai lokacin da Mai girma gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya yi kira ga jama’a su nemi hanyar kare kansu.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

Tun a lokacin maganganun Rt. Hon. Aminu Bello Masari suke ta jawo surutai. Wasu suna ganin gaza war gwamnati da jami'an tsaro ya jawo wannan kiran.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Dodon Wawa

An jefa mutanen Kankara a makoki ne yayin da jama’an garin New Bussa a kasar Borgu suke jimamin dauke Dodon Wawa, Alhaji Mahmud Aliyu a jiya.

Rahotanni sun ce an sace basaraken ne daga fadarsa a ranar Asabar. Rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun tabbatar da auku war wannan mummunan labari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel