Bamu yi sulhu da Fulani ba: Yan Irigwe da akewa zargin kashe matafiya a Jos

Bamu yi sulhu da Fulani ba: Yan Irigwe da akewa zargin kashe matafiya a Jos

  • Yan garin Irigwe sun ce ba zasu yi wani zama da Fulani da ya sabawa abinda suka yanke shawara ba
  • Gwamnatin jihar Plateau ta shirya zaman sulhu a gidan gwamnati dake Jos
  • An yi asarar rayuka da dama sakamakon rikice-rikice a jihar Plateau makonnin baya-bayan nan

Jos - Kungiyar cigaban garin Irigwe (IDA) tace ta karyata labarin cewa an yi zaman sulhu tsakaninta da Fulani Makiyaya a gidan gwamnatin jihar Plateau dake Jos.

A jawabin da Sakataren kungiyar, Danjuma Auta, ya saki, yace da ba zasuyi martani kan wannan ba amma kawai sun yi tunanin akwai bukatar bayyanawa al'umma gaskiya, rahoton Leadership.

A cewarsa, al'ummar Irigwe basu suyi wani zaman sulhu da kowa ba kuma ba zasu yi wani zaman sulhu ba sabanin abinda al'ummarsa suka yanke shawara.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

Yace:

"Saboda haka muna kira ga 'yayanmu suyi watsi da wadannan labaran karyan, duk da cewa muna kira ga kowa ya cigaba da addu'a domin samar da zaman lafiya a gari."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bamu yi ba, kuma ba za muyi sulhu da Fulani ba: Yan Irigwe da akewa zargin kashe matafiya a Jos
Bamu yi ba, kuma ba za muyi sulhu da Fulani ba: Yan Irigwe da akewa zargin kashe matafiya a Jos
Asali: Facebook

An zargi matasan Irigwe da kisan mutum 20 makonnin baya

Wasu yan bindiga da ake zargin matasan Irigwe ne sun kai wa Musulmai matafiya 90 hari a jihar Plateau ranar Asabar, akalla mutum 22 sun mutu, yan sanda suka tabbatar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya bayyana cewa wasu matasa Kirista yan garin Irigwe suka kaiwa Musulman farmaki, rahoton Channelstv.

Jami'in yan sandan ya kara da cewa mutum 21 sun tsallake rijiya da baya.

Buhari ya girgiza, ko abinci ya kasa ci: Pantami

Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana cewa shugaban Muhamadu ya kasa cin abinci ranar da aka kai hari kan Musulmai a Jos.

Kara karanta wannan

Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani

A ziyara ta musamman da ya kaiwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a madadin Buhari, Pantami yace Buhari ya yi matukar bacin rai kan abinda ya faru har abinci ya gaza ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel