Gwamnan Najeriya ya ba ma’aikata wa’adin kwanaki 14 don yin allurar korona

Gwamnan Najeriya ya ba ma’aikata wa’adin kwanaki 14 don yin allurar korona

  • Gwamnatin jihar Ondo ta ba da sanarwar cewa za ta aiwatar da sabbin matakai don hana yaduwar cutar ta COVID-19
  • An shawarci ma’aikatan gwamnati a jihar da su kasance masu bin ƙa’idar COVID-19
  • Cutar korona ta sake bulla a wasu jahohi a fadin kasar nan

Gwamna Rotimi Akeredolu ya umarci ma’aikatan gwamnati a jihar Ondo da su yi rigakafin COVID-19 a cikin makonni biyu.

An bayar da wannan umarnin ne a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba, a cikin wata takardar da OJ Afolabi, babban sakatare, mai kula da harkokin hidima ya sanya wa hannu, a madadin shugaban ma’aikatan gwamnati na Ondo, jaridar ThisDay ta ruwaito.

Gwamnan Najeriya ya ba ma’aikata wa’adin kwanaki 14 don yin allurar korona
Gwamnan Najeriya ya ba ma’aikata wa’adin kwanaki 14 don yin allurar korona Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Gwamnatin ta bayyana cewa daga yanzu ma’aikatan gwamnati za su bayar da katunan shaidar rigakafi kafin a ba su damar shiga wasu wuraren.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

Sanarwar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

''Gwamnatin jihar Ondo ta sanya allurar rigakafin COVID-19 ya zama tilas ga dukkan ma'aikatan jihar.
“A cikin daftarin gwamnati wanda Sakataren dindindin na harkokin ma’aikaya, Mista O.J. Afolabi, a madadin shugaban ma’aikata, gwamnatin jihar ta ba ma’aikatan gwamnati a jihar makonni biyu su dauki allurar rigakafin.”

A wani labari na daban, hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su katse hanyoyin sadarwarsu a jihar Zamfara, Daily Nigerian ta ruwaito.

A daya daga cikin wasikun da aka aike wa kamfanonin, mataimakin shugaban hukumar Umar Danbatta a ranar Juma'a 3 ga watan Satumba ya ce matakin na daya daga cikin dabarun da jami'an tsaro ke bi na dakile 'yan bindiga da ke addabar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel