Da duminsa: Yan bindiga sun kashe Kanin Mai Sahara Reporters, Sowore

Da duminsa: Yan bindiga sun kashe Kanin Mai Sahara Reporters, Sowore

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da mutum biyar a Edo
  • A wannan harin yan bindigan sun kashe dan'uwan mai kamfanin jaridar Sahara Reporters
  • Gwamnan jihar Edo ya lashi takobin damke wadanda suka aikata wannan

Edo - Yan bindiga sun bindige Olajide, wanda kani ne ga mai gidan jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, har lahira.

Sowore ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook ranar Asabar.

Dan jaridan ya bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kasheshi a hanyarsa daga jami'ar Igbinedion dake garin Okada, jihar Edo.

A cewarsa:

"Masu garkuwa da mutane makiyaya sun kashe kanina dake biye dani, Olajide Sowore, kusa da Okada a jihar Edo, yayinda yake dawowa daga jami'ar Igbinedion inda yake karatun ilmin magunguna."

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya aurar da diyarsa Hauwa ga dan Sarkin Azara

Da duminsa: Yan bindiga sun kashe Kanin Mai Sahara Reporters, Sowore
Da duminsa: Yan bindiga sun kashe Kanin Mai Sahara Reporters, Sowore
Asali: Facebook

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta tabbatar da kisan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Edo, Kontongs Bello, ya ce masu garkuwa da mutane sun kashe Olajide da misalin karfe 6:00 na safiyar Asabar, jaridar ta kuma ruwaito.

Hakazalika ya bayyana cewa sun yi garkuwa da wasu mutum biyar a yayin harin.

Yace:

“Ina tabbatar muku da cewa wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da misalin karfe 06:45 na safiya a hanyar Legas zuwa Benin ta hanyar Isuwa sun yi garkuwa da mutane biyar da ba a san ko su wanene ba sannan a cikin lamarin sun harbi wani Sowore Felix Olajide, dalibin karatun hada magunguna na Jami’ar Igbinedion Okada.
“An ajiye gawarsa a IUTH dakin ajiye gawa na Okada yayin da ake ci gaba da kokarin ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su. Ana ci gaba da aikin bincike da ceto.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel