Ba zan daina goyon bayan Shugaba Buhari ba, Korarren Ministar Lantarki Saleh Mamman

Ba zan daina goyon bayan Shugaba Buhari ba, Korarren Ministar Lantarki Saleh Mamman

  • Saleh Mamman yace ba zai daina goyon bayan Shugaba Buhari ba
  • Tsohon Ministan yace yana alfahari da ayyukan da yayi cikin shekaru biyu
  • Saleh ya fayyace maganar rashin lafiyar da yake fama da ita

Tsohon Ministan wutan lantarki, Injiniya Saleh Mamman, ya bayyana cewa ba zai daina goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba duk da ya koresa.

Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki kwana daya bayan shugaba Buhari ya sallamesa daga kujerarsa matsayin Minista a gwamnatinsa a shafinsa na Facebook.

Saleh Mamman ya ce har gobe ba zai daina goyon bayan manufofin Shugaba Muhammadu Buhari ba kuma ba zai daina goyon bayansa ba.

Ya godewa Buhari bisa damar da ya bashi na bada nasa gudunmuwar da cigabar kasa.

Kara karanta wannan

Saleh Mamman ya yi magana a Facebook, awa 24 bayan Buhari ya tunbuke shi daga Minista

Ba zan daina goyon bayan Shugaba Buhari ba, Korarren Ministar Lantarki
Ba zan daina goyon bayan Shugaba Buhari ba, Korarren Ministar Lantarki Saleh Mamman
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sale Mamman: Abin da yasa ban koma gidana ba tun bayan da Buhari ya kore ni

Sale Mamman, tsohon ministan makamashi, ya yi bayanin abin da yasa bai koma gidansa ba bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sallame shi daga aiki.

Wasu rahotanni sun ce an kwantar da ministan a asibiti bayan ya samu labarin cewa an kore shi.

Tsohon ministan ya amsa cewa tabbas ba shi da lafiya, amma ya ce tun makon da ta gabata ya ke shan magunguna saboda rashin lafiyan.

Ya ce:

"Tun kafin a sanar cewa an kore ni, ina fama da rashin lafiya. Ban tafi ofis ba tun farkon wannan makon."
"Jiya (Laraba) da yau (Alhamis) na sake komawa asibitin saboda a sake duba ni; kuma likitan ya bada umurnin cewa ina bukatar hutu don haka na tsaya a wuri daya domin in huta."

Kara karanta wannan

Sale Mamman: Abin da yasa ban koma gidana ba tun bayan da Buhari ya kore ni

Asali: Legit.ng

Online view pixel