Mahaifi ya ƙwace ƴar shi bayan ta haifa ƴaƴa 5 saboda miji ya ƙi biyan sadaki

Mahaifi ya ƙwace ƴar shi bayan ta haifa ƴaƴa 5 saboda miji ya ƙi biyan sadaki

  • Geoffrey Kakona ya lallaba har gidan auren diyar sa ya taso keyar ta daga gidan mijin ta saboda mijin ya ki biyan sadakin auren su
  • Yanzu haka ma’auratan su na da yara 5, babban cikin yaran yana da shekaru 10 a duniya yayin da karamin har yanzu a ke shayar da shi
  • A cewar mijin, ya na kokarin ganin ya tattara sadakin ya biya a watan Disamban wannan shekarar, amm sai sirikin sa ya mamaye sa ya dauke diyar sa

Uganda - Mahaifin matar wani Laban Sabiti, mai shekaru 29, mazaunin kauyen Bashayu a wuraren anguwar Rubanda a kasar Uganda, ya tasa keyar diyarsa mai yara 5 zuwa gida. Yanzu haka cikin yaran akwai jariri mai watanni 13 a duniya.

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

Sirikin sa, Geoffrey Kakona, mazaunin kauyen Karima a anguwar Kanungu, ya amshe diyarsa bayan Sabiti ya kasa biyan sadakin auren ta, LIB ta ruwaito.

Uba ya kwace 'yar shi bayan ta haifa 'ya'ya 5 saboda miji ya ki biyan sadaki
Uba ya kwace 'yar shi bayan ta haifa 'ya'ya 5 saboda miji ya ki biyan sadaki. Hoto daga The Nation
Asali: Facebook
“Tabbas na dauki tsawon lokaci ban biya sadakin auren mu ba amma ina kokarin biya a watan Disamban wannan shekarar. Na yi mamakin yadda siriki na ya zo ya dauke min mata ta, Prize Twikirize, duk da na yi masa bayanin ina da niyyar biyan sadakin,” cewar Sabiti, lokacin da ya shigar da karar wurin ‘yan sanda.

Babban dan Sabiti ya kai shekaru 10 a duniya yayin da karamin har yanzu nono ya ke sha.

George Williams Katatumba, ya lura da yadda Sabiti ya ki daraja al’adar sa, kuma a ka’ida babu irin wannan auren.

“Tunda har haihuwa ta yi da Sabiti, dole ne a ci shi tarar garin gero, jarkar mai da tunkiya ko kuma akuya,” a cewar Katatumba.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya sabunta naɗin magatakardan hukumar TRCN

Babban dan sandan yankin Mbarara, Steven Tumwiine, ya ce sam ba za ta sabu ba, gwamnati ta hana biyan sadaki.

“Bisa dokar kasar Uganda, babu wani sadaki ga auren duk wanda ya kai shekaru 18 a duniya, kuma kowa ya na da damar auren wanda ya ke so. Don haka mahaifin Twikirize ya shiga hakkin diyar sa. Sannan ya shiga hakkin jikokin sa ta hanyar raba su da iyayen su.”

Dokar da kotu ta yanke a shekarar 2017, ta hana biyan sadaki ga ma’aurata. Sannan kotu ta amince dari bisa dari da auren.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, tun farkon 2015, kotun koli ta bayar da dokar a kan mayar wa miji sadakin aure ba rabuwar aure bane, kuma hakan ya saba wa doka.

Sale Mamman: Abin da yasa ban koma gidana ba tun bayan da Buhari ya kore ni

A wani labari na daban, Sale Mamman, tsohon ministan makamashi, ya yi bayanin abin da yasa bai koma gidansa ba bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sallame shi daga aiki, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

Wasu rahotanni sun ce an kwantar da ministan a asibiti bayan ya samu labarin cewa an kore shi.

Amma, a wata hirar wayar tarho da ya yi da BBC Hausa, Mamman ya karyata rahoton.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel