Allah ne ya haɗa mu: Kwankwaso ya magantu kan haɗuwar shi da Ganduje

Allah ne ya haɗa mu: Kwankwaso ya magantu kan haɗuwar shi da Ganduje

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Allah ne ya hada shi da Gwamna Ganduje a filin jirgi
  • An ga hoton 'yan siyasan biyu da ba su ga maciji a filin jirgi, lamarin da ya janyo maganganu daban-daban daga jama'a
  • Sai dai Kwankwaso ya ce hanya ce kawai ta hada su daga Abuja, kuma bayan gaisawarsu kowa ya kama gaban shi

Kano - Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bada labarin yadda suka hadu da wanda ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, manyan 'yan siyasan biyu sun hadu a filin sauka da tashin jiragen sama da ke Abuja kuma sun hau jirgi daya zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Allah ne ya haɗa mu: Kwankwaso ya magantu kan haɗuwar shi da Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da Alhaji Rabiu Kwankwaso a wurin wani taro. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Su biyun sun yi aiki tare a shekaru masu yawa da suka gabata, sun kuma raba jiha tun bayan da Ganduje ya gaji kujerar Kwankwaso a shekarar 2015.

A yayin da Kwankwaso ya jagoranci jihar Kano, Ganduje ne mataimakinsa tsakanin 1999 zuwa 2003.

Kwankwaso ya yi aiki karkashin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin ministan tsaro.

Amma kuma bayan sake zaben Kwankwaso a shekarar 2015, ya sake daukan Ganduje a matsayin mataimakinsa.

A yayin zantawa da BBC hausa, Kwankwaso ya ce ya kwashe kusan sa'a 1 a wurin jira bayan an sanar da shi cewa Ganduje yana kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin.

"Na ce ba komai, Allah ne ya hada mu. Wurin kamar tasha ce, babu wanda zai ce wa wani ya zo ko kada ya zo. Ya zo, mun gaisa da juna.

Kara karanta wannan

An sassauta doka: Mazauna Jos sun garzaya kasuwanni domin sayen kayan abinci

“Mun hau jirgi daya kuma mun sauka a filin jirgi na Kano. Na zauna a gaba, don haka ni na fara sauka. Na gaida mutanen shi kuma na kama hanyata zuwa gida na," Kwankwaso yace.

A lokacin da aka tambaye shi ko ya shawarci gwamnan kamar yadda ya saba kalubalantar wasu daga cikin tsare-tsarensa, Kwankwaso ya ce:

"A matsayinmu na Musulmi, ba sai muna jam'iyya daya ba za mu gaisa da juna. Shiyasa muka gaisa kuma na zauna a mazauni na, shi ma haka."

Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa

A wani labari na daban, sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya ce ana tsaka mai wuya a harkar tsaro shugaba ya hau karagar mulki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Baba a lokacin da matsalolin IPOB suka addabi kowa a watan Afirilu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a lokacin ne suka yi ta banka wa ofisoshin ‘yan sanda wuta suna balle gidajen gyaran hali suna sakin fursunoni.

Kara karanta wannan

Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje

Asali: Legit.ng

Online view pixel