Yan fashi sun sace Tirelan Dangote dauke da buhuhunan Siminti 900

Yan fashi sun sace Tirelan Dangote dauke da buhuhunan Siminti 900

  • Ba tsoro wasu barayi suka sace tirela mai dauke da buhuhunan Siminti 900
  • Sun kwace motar ne hannun direban da yaron motarsa a Edo
  • Tuni jami'an yan sanda sun yi ram da su kuma an kwace motar

Hukumar yan sanda a jihar Delta ta kwato Tirelan Dangote mai dauke da buhun Siminti 900 da wasu barayi suka sace ranar Talata a garin Okpella, jihar Edo.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Bright Edafe, a jawabin da ya saki ranar Alhamis a Asaba yace an gano motar ne a kauyen Aniegele inda aka damke barayin bayan kure musu gudu, rahoton Premium TImes.

Yace:

"A ranar 31 ga Agusta, 2021, misalin karfe 9:30 na safe, jami'an yan sandan yakin Illah na kan sintiri a titin Illah-Asaba suka samu labari daga wani direban Dangote cewa an sace Tirelarsa dauke da buhunan Siminti 900."

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

"Yace yayinda yake shirin ajiye motar mai lamba DAS 690 Zy a Okpella a Edo, wasu mutum hudu rike da makamai suka fito daga daji suka jefashi da yaran motarsa cikin daji."

Yan fashi sun sace Tirelan Dangote dauke da buhuhunan Siminti 900
Yan fashi sun sace Tirelan Dangote dauke da buhuhunan Siminti 900 Hoto: Labourers
Asali: UGC

A cewarsa, ba tare da bata lokaci ba jami'an yan sanda suka bazama aiki kuma suka gano inda aka boye motar a Aniegele.

Yace barayin na ganin motar yan sanda suka gudu daji amma yan banga suka kure musu gudu suka kamasu.

Kakakin yan sandan ya cigaba da cewa:

"Yan bangan sun bi su cikin daji kuma sun damke mutum hudu masu sunaye: Ozioma Umez, Uchenna Idenyi, Chibuike Nwamgbo, da Chiolada Nomha."
"An kamasu da adduna biyu. Ana gudanar da bincike."

Barayi sun mayar da kuɗaɗen da suka sata bayan an kai su gaban ƙasurgumin boka

Kara karanta wannan

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

A wani labarin kuwa, wasu barayi da suka saci Ghc10,000 daga wurin wani bawan Allah sun lallaba sun mayar da kudin bayan ya kai karar aiki wurin wani kasurgumin boka a gidan tsafin sa na Borkor Bullet Hanson da ke wuraren Volta a Ghana.

Kamar yadda Revival FM suka wallafa a Facebook, da farko bokan ya gayyaci barayin guda 5 zuwa gidansa na tsafi na Borkor Bullet Hanson don su yi bayani, amma suka murje idanunsu suka ce ba su saci kudin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel