'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger

'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger

  • 'Yan sanda da ke da alhakin yaki da 'yan bindiga sun sheke Buba Baromi, mai bai wa 'yan bindiga bayanan sirri a Niger
  • Mafarautan Niger ne suka jagoranci tawagar 'yan sanda har cikin dajin Damba inda Baromi ke jinyar raunin harbi
  • Ba bayanai kadai Baromi ke bai wa 'yan bindiga ba, yana jagorantarsu zuwa inda za su kai farmaki tare da nuna musu jama'a

Niger - Jami'an rundunar yaki da 'yan bindiga ta 'yan sandan jihar Niger sun bindige gagararren mai kai wa 'yan bindiga bayanai, Buba Baromi.

An sheke Baromi ne a wata maboyarsa da ke dajin Damba na jihar Niger, PRNigeria ta ruwaito.

'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger
'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

PRNigeria ta tattaro cewa, wasu mafarautan yankin sun jagoranci 'yan sanda maboyar Baromi inda ya ke jinyar wani harbin bindiga da aka yi masa yayin wata arangama da yayi da jami'an tsaro a baya.

Kara karanta wannan

Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani

Wani jami'in sirri da aka yi aikin da shi, ya sanar da PRNigeria cewa, Baromi ba bayanai kadai yake kai wa 'yan bindiga ba, har jagorantarsu yake yi zuwa wurin da za su kai farmaki kuma su sace jama'a.

"Shehu Buba Baromi gagararren mutum ne da ke samarwa da miyagun 'yan bindiga bayanai tare da jagorantarsu zuwa inda za su kai farmaki, su sace jama'a ko kuma satar shanun jama'a.
“A tsakiyar watan Augusta, ya jagoranci wasu miyagu masu satar shanu kuma sun kaddamar da hari a kauyen Dogon Fadama inda mutane suka rasa rayukansu.
“A wata arangama da 'yan sanda da yayi, ya samu rauni daga harsashi kuma ya tsere zuwa dajin Damba inda ake jinyarsa.
“Amma kuma, a ranar Talata, 'yan sanda sun tsinkayi dajin kuma sun yi musayar wuta da 'yan bindiga da ke jinyarsa, lamarin da yasa aka sheke shi a take.

Kara karanta wannan

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

“An adana gawarsa a wani asibiti saboda wadanda ya cutar da wadanda suka san gagararsa su tabbatar da mutuwarsa," yace.

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

A wani labari na daban, shugabannin jam'iyya mai mulki ta APC, sun ce kusan makuden kudi da suka kai tiriliyan daya da kadarori shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwato daga mahandama bayan hawansa kujerarsa a APC, Daily Trust ta wallafa.

A wata takarda da aka fitar a ranar Alhamis, tsohon sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar, Lanre Issa-Onilu, mamba na kwamitin rikon kwarya, Barista Isma'il Ahmed, hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi da darakta janar na zauren gwamnonin jam'iyyar, Salihu Lukman, sun ce an samu manyan nasarori.

Kamar yadda takardar ta shaida, gwamnati ta na amfani da kudaden da ta gano ne wurin ayyuka na musamman da kuma sanya hannun jari ko kuma a shigar da su cikin kasafin ko wacce shekara.

Kara karanta wannan

Abinda ka raina: Ana sayar da jakar 'Ghana-Must-Go' N860k a Amurka

Asali: Legit.ng

Online view pixel