Abubuwa 2 da Shugaban kasa ya duba kafin ya yi waje da Sabo Nanono da Saleh Mamman daga ofis

Abubuwa 2 da Shugaban kasa ya duba kafin ya yi waje da Sabo Nanono da Saleh Mamman daga ofis

  • Femi Adesina ya yi bayanin dalilin sauke Ministocin noma da na lantarki
  • Hadimin shugaban kasar yace Buhari ya damu da harkar abinci da wuta
  • Adesina yace za a maye guraben jihohin Kano da Taraba a majalisar FEC

Abuja - A ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba, 2021, Fadar Shugaban kasa ta yi karin haske a kan abin da ya sa Muhammadu Buhari ya kori Ministoci.

Punch tace hadimin shugaban kasar Najeriya, Femi Adesina ya yi wannan bayani a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a ranar Alhamis.

Mai taimaka wa shugaban kasar wajen yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina yace Buhari yayi la’akari da batun abinci da sha’anin lantarki.

Femi Adesina da ya bayyana a shirin ‘Sunrise Daily’ na tashar Channels Television, ya bayyana cewa shugaban kasar bai wasa da wadannan abubuwa.

Kara karanta wannan

Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

Rashin wuta da tsadar abinci

A cewar Adesina, akwai ranar da shugaban kasar yayi ta nanata cewa ina ma za a iya shawo kan matsalar wutar Najeriya saboda yadda ya damu da batun.

Haka zalika, hadimin yake cewa Mai gidansa yana kwana da halin da al’umma ke ciki na yunwa da wahala, yace yana da labarin abin da ke faru wa a ko ina.

Sabo Nanono
Sabo Nanono a ranar karshe a ofis Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Adesina ya bayyana cewa Ministocin rikon kwaryan da aka nada ba su gaza a mukamansu ba, sai dai an ga za su iya aiki ne a wasu ma’aikatun na dabam.

Abin da sauya-sauyen yake nufi

“Watakila shugaban kasa ya ga za su iya aiki a ko ina ne a gwamnatin. Bai nufin sun gaza, shiyasa aka maye guraben su a gida. Kuma za a nada wasu sababbin Ministocin.”

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

“Dalili kuwa shi ne tsarin mulki da dokar kasa sun ce dole kowace jiha ya zama ta na da Minista.”

Hadimin ya kuma ce idan sauye-sauyen da aka yi ya jawo wata jiha ko jihohi biyu ba su da Ministoci, dole za a fitar da sababbin mukamai a gwamnati.

Tsohon ‘dan jaridar yace nadin Ministoci ba sarautar gargajiya ba ne don haka shugaban kasa zai yi tunani, ya nada wanda ya ga shi ne ya dace da mukamin.

Buhari ya yi daidai?

Ku na da labari cewa labarin sallamar Ministocin gona da na wutar lantarkin ya yi wa wasu masu ruwa da tsaki da kungiyoyi masu zaman kansu dadi.

Daga mai yabon shugaban kasa, sai masu cewa ai ya kamata ace an yi waje da su tuni. Daga cikinsu akwai Farfesoshi Sam Amadi da Kingsley Moghalu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel