Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

Tsokacin Edita: Najeriya kasa ce da tafi kowacce kasa yawan mutane a fadin Afrika, wannan yasa ake sanya ta jerin kasashe masu girma. A bangare guda, duba da yadda gwamnatin Najeriya ke fafutukar inganta tattalin arziki, rahotanni kan fito don nuna yadda mazauna a kasar ke fama da talauci. Wannan rahoton ya yi tsokaci kan wasu daga cikin matsalolin.

Najeriya - Wani rahoton Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama da Tattalin Arzikin Kasa (SERAP) ya ce ‘yan Najeriya miliyan 27 ne ke samun abin da bai kai Naira 100,000 ba a shekara, inji TheCable.

Kungiyar, a ranar Alhamis 2 ga watan Satumba, ta kaddamar da rahoto mai taken ‘Annobar da aka Manta da Ita: Yadda Cin Hanci da Rashawa a bangaren Lafiya, Ilimi, da Ruwa ke jefa 'yan Najeriya cikin talauci.'

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

A cewar rahoton, ‘yan Najeriya miliyan 56 na fama da talauci kuma 57.205 daga cikinsu galibinsu na dogaro da kansu ne.

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara
Yadda 'yan Najeriya ke fama da talauci | Hoto: voiceofarewa.ng
Asali: UGC

Rahoton ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"kashi 65 na mutanen da ke zaune a unguwannin marasa galihu suna zaune ne ko dai a gida mai daki daya ko biyu."

Ya kara da cewa kashi hudu na mutanen da ke cikin talauci suna da nakasa ta jiki.

Rahoton ya ci gaba da cewa:

“Cunkushewar yanayin rayuwa ya kara yawan bukatar ruwa. Kashi 19 ne kadai na mutanen da ke zaune a unguwannin talakawa ke samun ruwa daga gwamnati. Yawancin talakawa da suke samun ruwa daga gwamnati sun gamsu da ingancin ruwan da suka samu."

Dangane da samuwar ruwa, rahoton ya ce 79% na mutanen da ke cikin talauci ba sa samun ruwa daga gwamnati, 50.14% bisa dari sun dogara ne da rijiyoyi ko burtsatse don samar da ruwa.

Kara karanta wannan

NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

A bangare guda, 23.96% cikin dari ne suke samun ruwa daga koguna ko kududdufai; 10.51% suke samun ruwa daga gidajen makwabta, 1.54% kuma cikin dari suke samun ruwa daga wasu hanyoyin.

Cin hanci da rashawa ke jefa talakawa cikin matsanancin talauci da matsin rayuwa

Rahoton na TheCable ya ce abubuwa kamar zamba cikin kasafin kudi, zamba na sayayya, almubazzaranci da kudi, da sauran ayyukan da ba bisa ka’ida ba a fannin ruwa, ilimi, da kiwon lafiya su suke ci gaba da hana samar da abubuwa masu inganci ga ‘yan Najeriya.

“Talakawa ne ke cutuwa ba masu cin hanci da rashawa ba a fannonin kiwon lafiya, ilimi da ruwa. Jihohi ba su da takardun manufofi don taimakawa mutanen da ke cikin talauci ko mutanen da ke samun karancin kudi don samun isa ga kiwon lafiya, ilimi da ruwa."
“Ko da kuwa akwai, jami’an gwamnati da ke hidimar mutanen da ke zaune a unguwannin marasa galihu ba basu san da su ba.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Afghanistan ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus

“Cin hanci da rashawa yana ba da gudummawa ga talauci da sakamakon wahalar mutanen da ke zaune a cikin unguwannin marasa galihu.
"Zamba a kasafin kuɗi, zamba na siyayya, almubazzaranci da kudi tsakanin sauran ayyukan da ba bisa ka'ida ba, na haifar da gazawa wajen isar da ayyuka da suka hada da ilimi, ruwa da kiown lafiya.
"Duk da haka, mutanen da ke zaune a cikin unguwannin marasa galihu sun sha wahala sosai har suna ganin rashin isasshen ingantaccen aiki ba komai bane."

Rahoton ya kara da 61% na mutanen da ke zaune a unguwannin marasa galihu sun kasance tsakanin rashin samun ilimin boko har zuwa na sakandare.

Elijah Okebukola, babban jami’in bincike a Kwalejin Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ACAN), ya ce rahoton ya shafi jihohi biyu kowanne daga shiyyoyi shida na kasar nan.

Aikin Kwangila: Barazanar da Ma’aikatan Banki Ke Fuskanta Na Karancin Albashi

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

A wani rahoton, aiki a bankunan kasuwanci a Najeriya ya kasance aiki mai matukar cike takaici, kamar yadda wani matashi mai suna Basit ya koka kan yanayin aikin da yake a banki.

Matashin mai shekaru 28, wanda aka sakaya sunansa don kare bayanansa, yana aiki a matsayin jami'in bayar da kudi a bankin Fidelity a Najeriya tun shekarar 2015.

Shekaru shida, yana reshen Fidelity, yana aiki a matsayin da aka dauke shi, da karamin albashin Naira 68,000 ($ 165) a wata ba tare da karin girma ba.

Ba ka'ida ne aikin Basit ya rasa ba, tsarin da yake aiki a karkashinsa ne matsalar. A rubuce shi ba cikakken ma'aikaci bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel