Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa

Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa

  • Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Bala, ya ce ya amshi mulki a lokacin da yafi ko wanne cakwakiya
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a mukamin a watan Afirilun ana tsaka da matsalar IPOB
  • Sannan a lokacin ne aka yi ta banka wa ofisoshin ‘yan sanda wuta ana balle gidajen gyaran hali

Katsina - Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya ce ana tsaka mai wuya a harkar tsaro shugaba ya hau karagar mulki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Baba a lokacin da matsalolin IPOB suka addabi kowa a watan Afirilu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a lokacin ne suka yi ta banka wa ofisoshin ‘yan sanda wuta suna balle gidajen gyaran hali suna sakin fursunoni.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa
Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa. Hoto daga The Cable
Asali: Facebook

Yayin tattaunawa da gwamnan jihar Katsina, Bello Masari, Baba ya bayyana yadda ya fuskanci kalubale iri-iri kuma ya ke kan fuskanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, an horar da sababbin ‘yan sanda 20,000 don kara karfin hukumar.

“Na hau kujerar IGP a lokaci mai tsanani. Lokacin da na zo, ana ta kashe-kashe a kudu maso gabas da kudu kudu, an yi ta kashe jami’an tsaro ana lalata wuraren ayyukan su.
“Yayin da a ke kokarin daidaita kudu-kudu da kudu maso gabas, sai matsaloli suka fara yawa a arewa ta tsakiya da arewa maso yamma.
“Za mu kara horar da wasu jami’an daga ko wacce karamar hukuma a kasar nan. Bisa umarnin shugaban kasa, za mu horar da mutane 10,000 a 2020 da kuma wasu 10,000 a 2021, a cewarsa.

Dama Masari ya ce gwamnatinsa za ta kara kaimi wurin horar da wasu ‘yan sandan don gyara harkokin tsaron jiharsa.

Kara karanta wannan

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

Gwamnan jihar Katsina ya ce jami’an tsaro ba su da yawa kuma ba sa da isassun kayan aiki don bai wa jihar isasshen tsaro, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, za a hirar da ‘yan sa kai a ko wacce cikin kananun hukumomi 34 na jiharsa.

“A bisa fahimta ta, a kowacce karamar hukuma babu isassun ‘yan sanda, don a gaba daya jihar basu kai 3,000 ba.
“Idan an ce sun kai 3,000, ta ya za a yi su iya tsare mutane 200,000? Don hakan ya kamata a karo musu makamai kuma a kara horar da wasu.

Za mu hadu a kotu, Ortom ga Akume kan zargin dankara masa karya

A wani labari na daban, a ranar Laraba, Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya lashi takobin maka ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume a kotu don ya kawo hujjoji kwarara a kan zargin da ya ke yi wa mulkinsa.

Kara karanta wannan

A huɗubar Juma'a, Sheikh Nuru Khalid ya caccaki Buhari, yace ya bar ƴan bindiga suna mulki

Daily Trust ta ruwaito cewa, Ortom ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Makurdi inda ya zargi ministan da lailayo karya ya na maka masa a wata hira da aka yi da shi a Abuja.

Akume ya shawarci EFCC da ICPC inda yace su yi bincike mai tsanani a kan gaba daya dukiyar da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar Binuwai tun daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel