Harin NDA: Rundunar sojin Najeriya ta ki bayyana halin da Manjon da aka sace ya ke ciki

Harin NDA: Rundunar sojin Najeriya ta ki bayyana halin da Manjon da aka sace ya ke ciki

  • Rundunar soji ta ki bayar da bayanai a kan halin da Manjo Christopher Datong ya ke a hannun masu garkuwa da mutane
  • A makon da ya gabata ne masu garkuwa da mutane suke shiga har NDA da ke Kaduna suka kashe na kashewa suka yi garkuwa da shi
  • Bayan kwanaki kadan da faruwar hakan ne aka samu labarin ‘yan ta’addan sun bukaci naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa

Kaduna - Rundunar sojin kasa sun ki bayar da bayanai a kan halin da Manjo Christopher Datong wanda ‘yan ta’addan suka shiga har NDA da ke Kaduna suka yi garkuwa da shi a makon da ya gabata.

Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka shiga har gidajen sojoji da ke NDA inda su ka yi sanadiyyar ajalin sojoji guda biyu sannan su ka yi garkuwa da Datong.

Kara karanta wannan

Dakarun sojin Najeriya sun yi ram da 'yan bindiga 81, sun ceto mutum 33 a arewa maso yamma, DHQ

Harin NDA: Rundunar sojin Najeriya ta ki bayyana halin da Manjon da aka sace ya ke ciki
Hoton Manjo Christopher Datong, hafsan soja da miyagu suka sace a NDA. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan kwanaki kadan da farmakin, an samu labarai a kan yadda masu garkuwa da mutanen suka bukaci naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa yayin da wasu suka ruwaito cewa an hallaka shi.

A yayin da manema labari suka tambaya labarin halin da Manjon ya ke ciki a hedkwatar tsaro da ke Abuja a ranar Alhamis, Birgediya janar Benard Onyeuko, wanda shi ne mukaddashin darektan labaran soji ya ce hukumar soji za ta sanar da ‘yan Najeriya yadda a ke ciki, Daily Trust ta wallafa hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An wuce wannan wurin, mun san an dauki mataki. Muna jiran nasarar da za a samu,” a cewarsa.

Rashin kwazo: An gano sahihan dalilan da suka sa Buhari ya sallami Nanono da Mamman

A wani labari na daban, hankula sun tashi tun bayan ganin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke ministocinsa guda biyu daga majalisarsa kamar yadda Daily Trust ta gano.

Kara karanta wannan

Gidaje 5 na hafsoshin soja 'yan bindiga suka balle a NDA Kaduna

A jiya, shugaban kasa ya sanar da korar ministan noma da bunkasa karkara, Alhaji Sabo Nanono da kuma ministan wutar lantarki, Injiniya Sale Mamman yayin taron majalisar zartarwa a karshen kowanne mako.

Wannan ne karo na farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tauna aya don tsakuwa ta ji tsoro tunda ya hau mulki a 2015. Ya dawo ya cigaba da ayyuka tare da ministocinsa tun na farko da aka zabe shi a 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel