Rashin tsaro: Gwamnatin Kaduna ta haramta safarar dabbobi daga wasu jihohi

Rashin tsaro: Gwamnatin Kaduna ta haramta safarar dabbobi daga wasu jihohi

  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta hana safarar dabobbi zuwa cikin jihar daga wasu jihohi
  • Gwamnatin ta bayyana cewa an dauki matakin ne domin inganta tsaro
  • Ta kuma bayyana cewa duk wanda aka kama yana saba dokar zai fuskanci hukunci

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta safarar dabbobi zuwa cikin jihar da kuma fita da su daga ranar 2 ga watan Satumba 2021, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da gwamnatin jihar ta dakatar da kasuwar mako da sayar da man fetur a cikin jarkoki a kananan hukumomi biyar.

Rashin tsaro: Gwamnatin Kaduna ta haramta safarar dabbobi gaga wasu jihohi
Rashin tsaro: Gwamnatin Kaduna ta haramta safarar dabbobi gaga wasu jihohi Hoto: The Punch
Asali: UGC

Gwamnatin jihar ta kuma jadadda cewa haramcin da ta sanya na yanke itatuwa a kananan hukumomi bakwai a wani bangare na matakan tsaro don yanke hanyoyin samar da kaya da mai ga 'yan ta'adda yana nan, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Niger ta rufe kasuwannin shanu, ta takaita yawo a babura

Wata sanarwar da Kwamishinan Tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba ta ce haramcin ya zama dole bayan tattaunawa mai zurfi da zurfafa bitar tsaro.

Aruwan ya ce:

“Wannan haramcin ya kuma hana safarar dabbobi zuwa jihar Kaduna daga wasu jihohi. Haramcin duka ya fara aiki nan take, daga yau 2 ga Satumba 2021.
“Gwamnatin tana kuma son sake nanata cewa safarar jakuna zuwa jihar laifi ne kuma duk wanda aka samu da hannu a ciki za a hukunta shi yadda ya dace.”

Sanarwar ta kuma dakatar da kasuwar Kawo ta mako -mako, wacce galibi ana yin ta kowace Talata a karamar hukumar Kaduna ta Arewa kuma ya fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta haramta cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomi biyar

Ya kara da cewa:

“Gwamnatin Jihar Kaduna tana son nuna cewa umarnin da suka gabata na dakatar da kasuwannin mako -mako, da siyar da mai a cikin jarkoki a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da Kajuru, tare da hana sare bishiyoyi don katako, itace da gawayi da sauran dalilan kasuwanci a Birnin Gwari, Kachia, Kajuru, Giwa, Chikun, Igabi da Kauru, har yanzu suna kan aiki.”

Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar

A baya mun kawo cewa gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.

Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.

Aruwan ya ce an bada sanarwar ne bayan gwamnatin ta gana da kungiyar masu sayar da itatuwa, katako, da gawayi a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel