Tunanin halin da yan gudu hijra ke ciki na hanani kuzari lokacin kwanciyar aure: Ortom

Tunanin halin da yan gudu hijra ke ciki na hanani kuzari lokacin kwanciyar aure: Ortom

  • Gwamnan Benue ya bayyana rashin jin dadinsa kan halin da yan gudun hijran jiharsa ke ciki
  • Ortom yace ko kuzari bai iyawa cikin daki da matarsa idan ya tuna da su
  • Hadimar Buhari, Lauretta Onochie, tayi masa isgili kan wannan maganar da yayi

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana fushinsa kan yadda lamarin tsaro ya tabarbare a Najeriya wanda hakan ya sabbaba karuwar mutane a sansanin gudun Hijra.

Gwamnan yace bai samun kwanciyan hankali kuma bai samun isasshen bacci da dare idan ya tuna da wadanda ke sansanin gudun Hijra da aka tilastawa guduwa daga muhallansu.

Ortom yace wannan na matukar shafan kuzarinsa idan yana tare da matarsa cikin daki lokacin kwanciyar aure.

Tunanin halin da yan gudu hijra ke ciki na hanani kuzari lokacin kwanciyar aure: Ortom
Tunanin halin da yan gudu hijra ke ciki na hanani kuzari lokacin kwanciyar aure: Ortom Hoto: Samuel Ortom

Kara karanta wannan

Benue: Masu ruwa da tsaki na APC sun nemi Buhari ya ayyana dokar ta baci

A bidiyon da ya yadu a Facebook yace:

"Ko ina kan matata na tuna mutanen da ke sansanin gudun Hijra..."

Martani kan haka, hadimar Buhari na sabbin kafafen yada labarai, Lauretta Onochie, ta ce Samuel Ortom ko cikin dakin matarsa bai da kokari.

Kalli bidiyon:

Za mu hadu a kotu, Ortom ga Akume kan zargin dankara masa karya

A bangare guda, a ranar Laraba, Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya lashi takobin maka ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume a kotu don ya kawo hujjoji kwarara a kan zargin da ya ke yi wa mulkinsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Ortom ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Makurdi inda ya zargi ministan da lailayo karya ya na maka masa a wata hira da aka yi da shi a Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Akume ya shawarci EFCC da ICPC inda yace su yi bincike mai tsanani a kan gaba daya dukiyar da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar Binuwai tun daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel