Rigingimu 10 da suka jawo Sabo Nanono da Saleh Mamman suka rasa kujerun Ministoci

Rigingimu 10 da suka jawo Sabo Nanono da Saleh Mamman suka rasa kujerun Ministoci

  • A makon nan aka ji an tsige Saleh Mamman da Sabo Nanono daga FEC
  • Wannan ne karon farko da Muhammadu Buhari ya kori wasu Minitsoci
  • Duk da kokarinsu, an yi ta samun sabani da Mamman da Nanono a ofis

Abuja - A ranar 1 ga watan Satumba, 2021, fadar shugaban kasa ta bada tabbacin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kori wasu Ministocinsa.

Wadanda wannan zazzagar ta shafa sune; Alhaji Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman wadanda ke rike da Ministocin gona da na wuta.

Daily Trust ta tattaro wasu laifuffukan da Sabo Nanono ya yi da rigingimun da aka yi da Mamman, har suka jawo aka kore su daga ofis.

Su menene zunuban Nanono?

Da farko Sabo Nanono ya yi yunkurin canza shugabannin kungiyar manoma ta kasa, AFAN, ya goyi bayan ‘yan taware, hakan ya jawo aka je kotu.

Kara karanta wannan

Rashin kwazo: An gano sahihan dalilan da suka sa Buhari ya sallami Nanono da Mamman

An kuma zargi tsohon Ministan noman da bada kwangilar Naira miliyan 30 domin a gina masallaci.

Har ila yau, Nanono ya samu kansa a matsala da zargin kashe har Naira biliyan daya domin yi wa tsohuwar ma’aikatar harkar gona kwaskwarima.

Sabo Nanono da Saleh Mamman
Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Rahoton yace Alhaji Nanono ya bada wasu kwangilolin shigo da hatsi daga waje, wannan ya taimaka wajen jawo farashin abinci ya kara tashi.

A karkashin jagorancin tsohon Ministan ne ICPC ta binciki ma’aikatarsa da zargin batar da N16b. Sannan kuma ya samu sabani da gwamnan CBN.

Saleh Mamman ya fusata SGF

Rikicin farko da Saleh Mamman ya shiga shi ne tsige shugabar REA, Damilola Ogunbiyi, wanda daga baya gwamnatin tarayya ta dawo da ita ofishinta.

Daga nan sai Ministan ya sallami Usman Gur Mohammed daga hukumar TCN a 2020. Bayan ‘yan kwanaki sai aka ji ya kori Dr Marilyn Amobi daga NBET.

Kara karanta wannan

Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

Sannan Mamman ya yi waje da Farfesa James Momoh daga NERC tun kafin wa’adinsa ya kare.

An samu sauyi a FEC

A jiya ne aka sauya wa karamin ministan muhalli waje zuwa ma'aikatar aikin gona yayin da karamin ministan ayyuka zai rike ma'aikatar wuta.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan kafofin watsa labarai, Femi Adesina ya sanar da hakan bayan an sallami wadannan Ministocin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel