‘Yan Majalisar PDP sun zargi Jami’an tsaro da hada-kai da ‘Yan bindiga a jihar Arewa

‘Yan Majalisar PDP sun zargi Jami’an tsaro da hada-kai da ‘Yan bindiga a jihar Arewa

  • Wasu daga cikin ‘Yan majalisar Benuwai sun caccaki Sanata George Akume
  • ‘Yan majalisar sun yi tir da kiran da Ministan yake yi a kan a sa dokar ta-baci
  • Wani ‘dan majalisa yace da hannun jami’an tsaro ‘yan bindiga suke yin barna

Abuja - ‘Yan majalisar wakilan tarayya da aka zaba a karkashin PDP a Benuwai, sun zargi jami’an tsaro da hada-baki wajen kashe-kashen da ake yi a jihar.

A wani taron manema labarai da ‘yan majalisar suka kira a garin Abuja, sun yi kaca-kaca da Ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume.

Jaridar The Cable ta kawo rahoto a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, 2021, tace Honarabul Mark Gbillah ya yi magana a madadin sauran takwarorin na sa.

‘Yan majalisa sun yi wa Akume rubdugu

Mark Gbillah mai wakiltar mazabar Gwer ta gabas da yamma a majalisar tarayya ya zargi George Akume da yin gum a lokacin da ake hallaka mutanensa.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar Nasarawa 3 sun tsallake rijiya da baya akan hanyarsu ta zuwa jana’iza

Rahoton yace hakan na zuwa ne bayan Ministan ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya sa dokar ta-baci a dalilin kashe-kashen da ake yi a Benuwai.

A jawabin ‘yan majalisar, sun nemi gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta dauka, na bada Naira biliyan 10 domin a share wa ‘yan gudun hijira hawaye.

Buhari 'dan Idoma
Buhari da su Akume a Benuwai Hoto: www.idomavoice.com
Asali: UGC

Honarabul Francis Ottah Agbo mai wakiltar mazabun Ado/Ogbadibo/Okpokwu ya yi magana a taron, inda yace da jami’an tsaro ake kashe mutanen yankinsa.

“Mu duba mu ga yadda fadar shugaban kasa za ta yi abin da ya dace a Benuwai, domin gwamna ba zai iya yin abin da ya zarce kokarin da yake yi yanzu ba.”

Da hadin-bakin jami’an tsaro?

“A zuwa daya, ‘yan bindigan nan suka taba kashe mutanen Izzi 130 a mazabar da nake wakilta, ya suka yi abin na su?

Kara karanta wannan

Benue: Masu ruwa da tsaki na APC sun nemi Buhari ya ayyana dokar ta baci

“Sun yi wannan sun ci nasara ne domin kuwa ma’aikatan tsaro suna hada-baki da su, suna taimaka masu da kariya!”

Francis Ottah Agbo yake cewa a yadda ake tafiya a haka, lamarin ya fi karfin gwamna Samuel Ortom.

Buhari: 'Yan majalisan Katsina sun koka

An ji ‘dan Majalisar Danmusa a Katsina, Hon. Aminu Garba Danmusa yana cewa ya rasa laifin da Katsinawa su ka yi wa shugaba Muhammadu Buhari, ake kashe su.

Aminu Garba Danmusa ya ce dola a daina boye-boye, a fada wa kai gaskiya domin gwamnatin APC ta ba su kunya duk da tulin kuri'un da suka bada a lokacin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel