Zamu shiga yajin aiki idan aka kara kudin wutan lantarki, NLC

Zamu shiga yajin aiki idan aka kara kudin wutan lantarki, NLC

  • Kungiyar NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki idan har aka kara kudin lantarki
  • Hukumar NERC ta umurci kamfanonin Discos da suyi karin kudin wuta daga ranar 1 ga Satumba
  • Yan Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu game da wannan labari

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta ce za ta ingiza dukkan ma'aikatan Najeriya shiga yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta aiwatar da karin kudin wutan lantarki.

NLC ta tunatar da Ministan Kwadago, Chris Ngige, cewa an yi yarjejeniya tsakanin kwadago da gwamnatin tarayya a ranar 28 ga Satumba, 2020.

A cewar NLC, an yi yarjejeniyar cewa ba za'a kara kudin wutan lantarki ba har sai kwamitin ta kammala tattaunawa kuma kowa ya amince da rahoton.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba, ya bayyana hakan ne don martani kan rahotannin cewa NERC ta bada umurnin kara kudin lantarki ranar 1 ga Satumba, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar ta baci, ta kulle dukkan makarantun jihar

Yace:

"Muna son sanar da ku cewa sakamakon jita-jita da muke ji, musamman a kafafen yada labarai cewa ana shirin baiwa kamfanonin raba wuta umurnin kara farashin wutan lantarki.
"Ku sani cewa idan gwamnati ta gaskata wadannan rahotanni ta hanyar kara farashin wuta, kungiyar kwadago zata shiga yajin aiki don kare hakkin ma'aikata."

Zamu shiga yajin aiki idan aka kara kudin wutan lantarki, NLC
Zamu shiga yajin aiki idan aka kara kudin wutan lantarki, NLC Hoto: NLC
Asali: Twitter

Bai kamata a kara farashin kudin wutan lantarki ba'a karawa ma'aikata albashi ba

Mataimakin shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC, Joe Ajaero, ya yi kira ga gwamnatin tarayya kada ta sake ta kara farashin kudin wutan lantarki.

Ajaearo ya bayyana hakan yayin hira da yan jarida a shirin Kakaaki na tashar AIT ranar Talata.

Dan kwadagon wanda shina Sakatare Janar na kungiyar ma'aikatan wutan lantarki ya ce ta wani dalili NERC zata kara kudin wuta bayyan ba'a karawa ma'aikata kudin albashi ba.

Kara karanta wannan

Survival Fund: Gwamnati ta raba wa 'yan Najeriya sama da miliyan 1 kudade N56.8bn

Ya kara da cewa kamfanonin raba wuta (Discos) na kokarin daurawa talakawa nauyin gazawarsu.

Za'a kara kudin wutan lantarki ranar 1 ga Satumba

Hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya (NERC) ta umurci kamfanonin raba wutar lantarki 11 (Discos) su kara farashin wuta fari daga ranar 1 ga watan Satumba, 2021.

Bisa wani takarda da jaridar TheNation tayi ikirarin gani yau, hukumar NERC ta baiwa kamfanonin damar kara kudin ne a wasikar mai taken "Sanarwan Karin Farashi."

Hakazalika an tattaro cewa a wani takarda mai lamba ”023/EKEDP/GMCLR/0025/2021, kamfanin raba lantarkin Eko (EKEDC), ya sanar da kwastamominsa cewa za'a yi karin kudin wuta daga ranar 1 ga Satumba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel