Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

  • Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fada abin da yasa ya sallami ministocinsa biyu
  • Shugaba Buhari ya ce ya sauya ministocin ne domin kawo 'sabbin jini' da nufin inganta ayyuka
  • Shugaban kasar ya kuma ce irin wannan canjin da ya yi zai cigaba da faruwa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya sallami ministoci biyu daga cikin yan fadarsa da ya zaba a ranar 21 ga watan Agustan 2019.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce bukatar 'sabon jini' ne yasa aka yi sauyin ministocin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya kori ministocinsa biyu
Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya kori ministocinsa biyu. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An yi gagarumin sauyi a majalisar Shugaba Buhari, an sallami ministoci 2 daga arewa

Legit.ng ta ruwaito cewa an sallami Muhammad Sabo Nanono, Ministan Noma da Raya Karkara da Sale Mamman, Ministan Makamashi.

An maye gurbin su da Dr Mohammed Mahmood Abubakar, Ministan Muhalali da Abubakar D. Aliyu, Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje.

Har wa yau, sanarwar ta ce sauyin ministocin wani abu ne da 'za a cigaba da yi' idan bukatar hakan ta taso.

Ya ce:

"Wannan muhimman matakan da aka dauka sun taimaka wurin dakile wuraren da ake samun nakasu tare da inganta ayyuka domin habbaka tattalin arziki da samarwa yan Nigeria ababen more rayuwa.
"Ya zama dole in yabawa 'yan fada na saboda jajircewa da juriya da suka nuna wadda ta taimakawa gwamnati gudanar da ayyukanta duk da bullar annobar COVID-19 jim kadan bayan rantsar da ku. Taron Majalisar Kolin Tarayya ta FEC ita ma ta tabu saboda an sauya yadda ake yin ta.
"Kamar yadda muka sani, canji abu ne wanda ya zama dole a kowanne harkokin rayuwa kuma a halin yanzu da wannan gwamnatin ke tunkarar wani mataki mai muhimmanci a zagonta na biyu, na gano cewa yana da muhimmanci in yi sauyin da zai inganta ayyuka da nasarorin da muka samu a baya."

Kara karanta wannan

Zulum Ya Ziyarci Faston Da Aka Kashe Ɗansa Yayin Rushe Coci a Borno Don Masa Ta'aziyya

Hotunan doya da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta raba wa manoma a matsayin tallafi ya janyo maganganu

A wani labarin daban, shugaban karamar hukumar Obanliku a jihar Cross Rivers, Evangelist Margaret Inde, ta bawa sabbin manoma tallafin doya da fatanya da adda, daya-daya a matsayin tallafi, rahoton LIB.

SaharaReporters ta ruwaito cewa Inde ta mika kayan tallafin ne yayin bikin cika shekaru 30 da kirkirar karamar hukumar da kuma bikin fitowar sabuwar doya ta bana da aka yi a ranar Juma'a 27 ga watan Agusta.

A wasu hotuna da suka bazu a dandalin sada zumunta, an gano shugaban karamar hukumar tana bawa mutanen yankin ta tallafin doya daya, da fatanya da adda.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel