Shugabannin PDP sun zauna da Goodluck Jonathan, sun roke shi ka da ya jefar da Jam’iyya

Shugabannin PDP sun zauna da Goodluck Jonathan, sun roke shi ka da ya jefar da Jam’iyya

  • Shugaban rikon kwarya na PDP, Yemi Akinwonmi ya ziyarci Goodluck Jonathan
  • Kwamitin sulhu na David Mark ya zauna da Gwamna Nyesom Wike a Fatakwal
  • Jam’iyyar PDP tana kokarin dinke barakar cikin gidan da take fama da shi a yau

Meye Abin da ya sa Yemi Akinwonmi ya kai wa Jonathan ziyara?

Abuja - A ranar Talata, 31 ga watan Agusta, 2021, shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP na kasa, Yemi Akinwonmi ya hadu da Goodluck Jonathan.

Jaridar Punch ta bayyana cewa Yemi Akinwonmi da ‘yan tawagarsa sun kai wa tsohon shugaban kasar ziyara jiya ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Kusoshin adawa a Kudu maso yamma, Daisi Akintan da Misis Helen Taiwo suka yi wa Akinwonmi rakiya inda suka yi kus-kus da Dr. Jonathan.

Rahoton yace tawagar ta nemi jin ta bakin Jonathan a kan yadda za a shawo kan matsalolin cikin PDP tare da rokonsa ya yi hakuri ya zauna a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

Me ya kai Kwamitin Mark ya je Fatakwal?

A daidai wannan lokaci kuma kwamitin yin sulhu da aka kafa a karkashin jagorancin Sanata David Mark da wasu mutane bakwai suka ziyarci Ribas.

The Nation tace kwamitin Mark ya tattauna da Mai girma gwamna Nyesom Wike a garin Fatakwal.

Shugabannin PDP
Atiku Abubakar da Goodluck Jonathan Hoto: theeagleonline.com.ng
Asali: UGC

Wannan kwamiti ya shafe kusan sa’o’i uku da rabi yana tattauna wa da Nyesom Wike, inda aka gabatar masa da wasu bukatu a madadin jam’iyyar PDP.

Daga cikin abin da kwamitin ya nema a wajen gwamna Wike shi ne ya tursasa wa ‘yan PDP su janye karar da aka kai Prince Uche Secondus gaban kotu.

Haka zalika David Mark da ‘yan kwamitinsa sun bukaci gwamnan Ribas ya bada shawarar yadda za a tafiyar da PDP, sannan ya yi sulhu da Uche Secondus.

Kara karanta wannan

Abin da tsohon Sojan Najeriya ya fada da ya tsokano DIA ta ke neman shi ruwa a jallo

Sauran ‘yan kwamitin sulhun sun hada da Tom Ikimi: Okwesilieze Nwodo; Halliru Mohammed, Sanata Enyinaya Abaribe da kuma Hajiya Inna Ciroma.

PCG ta na goyon-bayan Osinbajo a APC

Wasu daga cikin ‘Ya ‘yan kungiyar PCG sun ziyarci Katsina da Daura domin nemawa Farfesa Yemi Osinbajo goyon-bayan 'yan jam'iyyar APC a zaben 2023.

Kungiyar Progressive Consolidation Group tace Osinbajo ya fi dace wa ya karbi mulki. A kan wannan PCG ta hadu da gwamnann Katsina da Sarkin Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel