ISWAP ta yi ikirarin sheke sojin Najeriya 10, sace makamai da alburusai a Rann

ISWAP ta yi ikirarin sheke sojin Najeriya 10, sace makamai da alburusai a Rann

  • 'Yan ta'addan ISWAP sun yi ikirarin sheke sojojin Najeriya goma a mummunan harin da suka kai garin Rann
  • Kamar yadda takardar da 'yan ta'addan suka saki ta nuna, sun ce sun sace makamai tare da alburusai a harin
  • Ba a nan suka tsaya ba, sun kona barikin sojoji, tankuna, tare da raunata wasu sojojin inda wasu suka tsere

Rann, Borno - Mayakan ta'addanci na ISWAP wadanda ake kira da Boko Haram, sun yi ikirarin sheke sojojin Najeriya goma bayan farmakin da suka kai sansanin sojojin da ke Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno.

'Yan ta'addan ISWAP sun kai wa sojoji farmaki a garin da wuraren da aka sani da tallafin jama'a ta bangare daban-daban da yawansu a ranar Litinin.

ISWAP ta yi ikirarin sheke sojin Najeriya 10, sace makamai da alburusai a Rann
ISWAP ta yi ikirarin sheke sojin Najeriya 10, sace makamai da alburusai a Rann. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A wata takardar da Daily Nigerian ta samu daga kungiyar 'yan ta'addan, ta ce ta kashe sojojin Najeriya goma tare da raunata wasu.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun kwace Rann, sa'o'i bayan farmakin mayakan ISWAP

Da izinin Allah, mun kashe sojoji goma na Najeriya, mun raunata wasu masu yawa yayin da sauran suka tsere daga Rann a jihar Borno. A ganimar yaki mun samu makamai da alburusai.
Mun kone barikin, tankuna biyu kuma hankali kwance muka koma sansaninmu," ISWAP ta ce a wata takarda.

Daily Nigerian ta tattaro cewa hankula sun kwanta kuma komai ya koma daidai a garin Rann.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Christopher Musa ya tura dakarun soji garin domin su duba halin da ake ciki tare da kai daukin da ya dace.

Nasara daga Allah: Sojoji sun kwace Rann, sa'o'i bayan farmakin mayakan ISWAP

A wani labari na daban, mayakan ISWAP sun kai wa sansanin soji da ke Rann farmaki, hedkwatar aiwatar da mulkin karamar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno. Tazarar Rann zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya kai 350km.

Kara karanta wannan

'Yan ISWAP sun fatattaki mazauna daga gidajensu a jihar Borno zuwa kasar Kamaru

Majiya masu karfi sun sanar da Daily Nigerian cewa mayakan ISWAP sun isa garin ne da yawansu inda suka yi ta harbe-harbe.

Wasu mazauna yankin, musamman fararen hula sun yi ta tsere zuwa dazuka yayin da ma’aikatan jin kai suka yi ta tserewa wuraren Kamaru.

Sai dai labaran da suka riski Daily Nigerian sun tabbatar da cewa tun bayan farmakin komai ya dawo daidai a yankin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel