Shugabancin 2023: Jerin manyan 'yan PDP 3 da za su yi gasar neman tikitin Jam'iyyar

Shugabancin 2023: Jerin manyan 'yan PDP 3 da za su yi gasar neman tikitin Jam'iyyar

  • 'Yan siyasa a fadin kasar na gwagwarmayar ganin sun cimma nasara gabannin zaben 2023
  • Akwai wasu manyan 'yan siyasa da ake ganin za su sake tsayawa takarar neman tikitin shugaban kasa na PDP
  • Wadannan 'yan siyasa sune Bukola saraki, Atiku Abubakar da kuma Aminu Tambuwal

Yayin da zaben shugaban kasa na 2023 ke karatowa, 'yan siyasa a fadin jam’iyyun siyasa sun fara hararar tikitin jam’iyyarsu domin zama yan takara.

Ga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), akwai ikirarin cewa manyan sunaye za su sake fitowa kamar yadda aka yi a zaben 2019.

Shugabancin 2023: Jerin manyan 'yan PDP 3 da za su yi gasar neman tikitin Jam'iyyar
Atiku, Tambuwal da Saraki na cikin manyan 'yan PDP 3 da za su yi gasar neman tikitin Jam'iyyar a zaben shugaban kasa na 2023 Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Wasu daga cikin manyan jiga-jigan da ake sa ran za su fafata don neman tikitin takarar shugaban kasa na PDP su ne Bukola Saraki, Atiku Abubakar, da Aminu Tambuwal, duk da cewa har yanzu ba su nuna sha’awarsu a takarar ba.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar goyon bayan Osinbajo ta fara kamfen na kasa baki daya, ta ziyarci Gwamna Masari na Katsina

1. Atiku Abubakar

Tare da gogewarsa sosai a harkar jagoranci, da alama Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa, zai yi iya bakin kokarinsa don ganin ya dare kujerar mulki a 2023.

A zahirin gaskiya, akwai tsammanin haka musamman tsakanin magoya bayan Atiku na arewacin kasar, wanda kwanan nan daya daga cikinsu ya shaidawa Vanguard cewa dattijon dan siyasar zai fito takarar shugaban kasa ne saboda muradun 'yan Najeriya.

Sai dai wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023 ta gargadi Atiku da kada ya tsaya takarar kujerar, bisa zargin cewa ya yi watsi da jam’iyyar adawa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

2. Aminu Tambuwal

Kasancewar ya tara abokai da yawa a fadin tarayyar kasar, gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya kasance tawaga mai karfi da za a sanya idanu a kansa gabannin zaben.

Kara karanta wannan

Sarakunan jihar Legas sun bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu a takarar Shugaban kasa

Tambuwal na daya daga cikin wadanda ke more kyakkyawar alaka da tsohon shugaban sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

3. Bukola Saraki

2023 ba zai zama karon farko da tsohon shugaban majalisar dattawa zai bayyana burinsa na zama shugaban Najeriya ba.

Saraki, wanda a cikin tarihin siyasarsa ya rike mukamin gwamnan jihar Kwara, ya shiga wani rukuni na siyasa a Najeriya.

Wani memba a kwamitin NEC na PDP ya yi magana a kanshi cewa:

“Saraki zai yi yaki da sauran mutane bisa la’akari da goyon bayan da ya samu zuwa yanzu daga tuntubarsa na kasa baki daya. Zai yi takara."

2023: A karshe Tinubu ya samu daidai da shi yayin da jiga-jigan PDP suka marawa tsohon gwamna baya

A gefe guda, mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Bamaina da ke karamar hukumar Birnin Kudu ta Jigawa sun bukaci tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Jam’iyyar PDP na iya damka wa ‘Dan Arewa tikitin tsaya wa takarar Shugaban kasa

‘Ya’yan babbar jam’iyyar adawar kasar sun bayyana haka ne a wani karamin taro da aka yi a garin Lamido a ranar Talata, 31 ga watan Agusta, jaridar PM News ta ruwaito.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Dr. Ibrahim Babandi ya dage cewa lallai sai Lamido ya shiga takarar shugaban kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel