Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyara Fadar Shehun Borno, Ya Yi Magana Kan Mayakan Boko Haram Dake Mika Wuya

Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyara Fadar Shehun Borno, Ya Yi Magana Kan Mayakan Boko Haram Dake Mika Wuya

  • Shugaban sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, ya kai ziyara fadar mai martaba shehun Borno domin masa ta'aziyya
  • Lawan yace mika wuyan mayakan Boko Haram wata hanya ce mai kyau ta kawo karshen matsalar tsaro a yankin
  • Sanatan yace gwamnatocin jihohi zasu haɗa karfi da FG wajen ganin an yi abinda ya dace ga tubabbun

Borno - Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana cewa mika wuyan yan Boko Haram ga sojojin Najeriya cigaba ne mai kyau kuma ya kamata a karfafa musu guiwa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Lawan ya faɗi haka ne ranar Litinin, mako ɗaya bayan sojojin ƙasa da FG sun tabbatar da cewa mayakan Boko Haram na tururuwar mika wuya.

Wannan ya biyo bayan ruwan wuta da yan ta'addan ke sha daga rundunar sojin Operation Haɗin kai ta sama da ƙasa a yankin arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Mun yi sa'an samun Buhari matsayin Shugaban Kasa, Shehun Borno

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyara Fadar Shehun Borno, Ya Yi Magana Kan Mayakan Boko Haram Dake Mika Wuya Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin hakan zai iya kawo karshen Boko Haram?

Sanata Lawan yace mika wuyan yan ta'addan wata kyakkyawar hanya ce ta kawo karshen matsalar tsaro da aka shafe sama da shekara 10 a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin wata ziyarar ta'aziyya da yakai fadar mai martaba Shehun Borno, Abubakar Elkanemi, bisa rasuwar yayansa, kuma tsohon ministan harkokin waje, Sanata Lawan yace:

"Ina da yakinin gwamnatin tarayya da ta jihar Borno da gwamnatocin sauran jihohin arewa maso gabas zasu yi aiki tare don tabbatar da waɗanda suka mika wuya an yi musu abinda ya dace don canza rayuwarsu."
"Ya zama wajibi mu cigaba da ƙarfafa wa tubabbun yan tada kayar bayan guiwa tare da waɗanda ba da son ransu suka tuba ba, domin hakan zai kawo mana karshen ta'addancin da muke fama da shi."

Zaman lafiya da kwanciyar hankali zai dawo a Borno

Kara karanta wannan

Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

Sanatan yace kyakkyawar alaƙar dake tsakanin FG da gwamnatin Borno zai kawo karshen duk wata matsalar tsaro a jihar, kamar yadda premium times ta ruwaito.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta samar da duk abinda ake bukata na kuɗi da kayan aiki ga hukumomin tsaro don kawo karshen matsalar.

Lawan yace:

"Ba da jimawa ba majalisar tarayya ta amince da baiwa hukumomin tsaro zunzurutun kuɗi biliyan N800bn a cikin karin kasafin kuɗi na 2021."
"Shugaban ƙasa ya tabbatar mana da cewa zai sake bukatar baiwa hukumomin tsaron wasu kuɗaɗe a kasafin kuɗin shekara mai zuwa, wanda za'a gabatar mana a karshen watan Satumba Insha Allah."

A wani labarin kuma Tattalin Arzikin Najeriya Ba Zai Samu Cigaba Ba Idan Ba Mu Ciyo Bashi Ba, Gwamnatin Tarayya

Ministan kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, tace cigaban tattalin arziki na kashi 5.01% da aka samu a rukunin shekara na biyu, 2021 zai samu koma baya idan ba'a ciyo bashi ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Ministan tace bashin da gwamnati ke ciyo wa tana zuba shi ne a ɓangaren gina muhimmman ayyukan kasa dake samar da aikin yi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel