An sassauta doka: Mazauna Jos sun garzaya kasuwanni domin sayen kayan abinci

An sassauta doka: Mazauna Jos sun garzaya kasuwanni domin sayen kayan abinci

  • A Jos ta jihar Filato, bayan sassauta dokar hana fita an ga mazauna na garzayawa kasuwa domin sayayya
  • Rahotanni sun bayyana cewa, an bude bankuna, ka na wasu tashoshin mota a garin na Jos sun dawo aiki
  • A kan ga jami'an tsaro a wurare masu muhimmanci a garin domin tabbatar da zaman lafiya a sassa dabandaban

Filato - Mazauna birnin Jos sun garzaya kasuwanni don siyan kayan masarufi bayan Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Jos ta Arewa da safiyar yau Litinin 30 ga watan Agusta.

Gwamnan a cikin rahoton da suka ruwaito muku a baya ya bayyana cewa yanzu dokar hana fita daga za ta fara aiki ne daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe har sai an sake samun wata sabuwar ci gaba.

Kara karanta wannan

Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa

An ruwaito cewa abokan cinikayya da dama sun kuma garzaya zuwa wasu bankunan da suka bude don gudanar da hada-hadar banki.

Wakilin Daily Trust, wanda ya zagaya, ya ba da rahoton cewa masu shaguna da sauran cibiyoyin kasuwanci suna ci gaba da hada-hada.

Manyan da kananan tashoshin mota ma sun fara aiki.

Sassauta doka: Mazauna Jos sun garzaya kasuwanni domin sayen kayan abinci
Taswirar jihar Filato | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, lamura sun daidaita tare da ganin jami'an tsaro a wurare masu mahimmanci a garin.

Sanarwar dokar hana fitar ta awanni 24 ta biyo bayan kisan akalla ‘yan kabilar Anguta 37 a Yelwa Zangam na Jos ta Arewa a makon da ya gabata.

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an hukunta duk mutanen da aka samu da hannu dangane da hare-haren da aka kai kwanan nan a jihar Filato, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Gwamnatin Plateau ta sassauta dokar hana fita a wasu sassan jihar

An kai hare-hare kan mutane da dama a garin Jos, babban birnin jihar Filato, da sauran sassan kasar a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda ya yi sanadiyar kashe-kashen mutane da dama, yayin da wasu mazauna garin da dama suka samu raunuka.

Sakamakon hare-haren da aka kai a Jos wasu gwamnatocin jihohi sun kwashe 'yan asalin jihohinsu dake karatu daga jihar ta Filato.

Dokar hana fita na awanni 24: Mazauna Jos sun koka kan karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki

A wani labarin, mazauna garin Jos, a ranar Asabar, 28 ga watan Agusta, sun koka kan karancin kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki a yankunansu bayan sake sanya dokar hana fita na sa'o'i 24 a yankin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mazauna yankin sun kuma koka game da hauhawar farashin kayan abinci bayan umarnin.

Gwamnatin jihar ta sake sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 bayan kisan wasu ‘yan kabilar Anaguta a ranar Talata a unguwar Yelwa Zangam da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.

Kara karanta wannan

Dokar hana fita na awanni 24: Mazauna Jos sun koka kan karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel