Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje

Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje

  • Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce jihar Kano bata goyon bayan hallasta amfani da ganyen wiwi a Nigeria
  • Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da shugaban NDLEA, Buba Marwa, da jami'an hukumar suka kai masa ziyara a Kano
  • Ganduje ya kara da cewa babu wani dan majalisar Kano da zai goyi bayan halasta wiwi bugu da kari musulunci ya haramta kayan maye

Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, a ranar Litinin ya nuna rashin jin dadinsa kan yunkurin da ake yi na hallasta amfani da ganyen wiwi a Nigeria, The Nation ta ruwaito.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai murabus) da manyan jami'an hukumar suka kai masa ziyarar ban girma a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba

Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje
Shugaban NDLEA, Buba Marwa da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sanarwar da kakakin NDLEA, Mr Femi Babafemi ya fitar, ya ce gwamnan ya ce babu wani dan majalisar tarayya daga jiharsa da zai goyi bayan irin wannan yunkurin, LIB ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya ruwaito cewa ziyarar na NDLEA zuwa Kano na cikin shirin yakin da hukumar ke yi na ta'amulli da miyagun kwayoyi, WADA.

Ganduje ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar Kano bata goyon bayan sha a fataucin miyagun kwayoyi, addinin da ya fi wanzuwa a jihar na Islama shima ya hana sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Ya ce:

"Kano ce jihar mafi yawan yan majalisu a majalisar tarayya. Ina son in tabbatar maka babu wanda zai goyi bayan hallasta ganyen wiwi a cikinsu.
"Za kuma mu amince da bukatar ka na neman fili domin gina gidajen jami'an hukumar reshen jihar Kano."

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin a binciko wadanda suka kashe dan sanata

Marwa ya roki Ganduje kada ya goyi bayan halasta ganyen wiwi

Tunda farko, Marwa ya bukaci gwamnan kada ya goyi bayan duk wani yunkuri na halasta amfani da ganyen wiwi da wasu zababbun yan majalisa ke yi.

Ya ce a halin yanzu NDLEA na aiki tukuru don ganin ta takaita bazuwar haramtaciyar kwayar a Nigeria.

Ya ce halasta haramtaciyar ganyen zai janyo koma baya ga nasarar da hukumar ta samu kawo yanzu.

Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Edo ta ce za ta saka tsauraran matakai a bankuna, majami'u, masallatai da wuraren shagulgulan biki kan duk wanda bai nuna shaidar yin riga-kafin cutar korona ba daga watan Satumba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamna Godwin Obaseki na jihar ya sanar da hakan ranar Litinin yayin kaddamar da kashi biyu na riga-kafin cutar korona a Benin City.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

Ya ce cutar korona nau'in Delta na yaduwa sosai kuma tana cigaba da yaduwa a kowanne lokaci, lamarin da yasa dole jama'a su yi riga-kafin cutar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel