Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Zata Samar Wa Matasa Masu Digiri 20,000 Aikin Yi Mai Tsoka

Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Zata Samar Wa Matasa Masu Digiri 20,000 Aikin Yi Mai Tsoka

  • Gwamnatin tarayya zata saka matasa masu takardar digiri aiki na musamman na tsawon wata 12
  • Rahoto ya nuna cewa shirin zai kunshi matasa yan kasa da shekara 30 aƙalla 20,000 daga faɗin ƙasa
  • Ana sa ran shugaba Buhari zai sanar da lokaci da kuma yadda matasa zasu nemi shiga tsarin ranar Talata

Abuja - Ana tsammanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai yi wata sanarwa dangane da wani shiri na musamman na matasa masu digiri ranar Talata.

FG ta kirkiri shirin ne da nufin samarwa matasa yan Najeriya da suka kammala digiri 20,000 aikin yi a wasu ɓangarorin gwamnati da kamfanoni a faɗin kasa.

Rahoto ya nuna cewa aikin matasan (yan kasa da shekara 30) zai kwashe watanni 12, kuma za'a basu cikakken albashin masu digiri.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Zata Samar Wa Matasa Masu Digiri 20,000 Aikin Yi Mai Tsoka Hoto: @Buharisallau
Asali: Instagram

Gwamnatin tarayya na fatan aikin zai taimaka wajen kimtsa matasan da suka kammala karatu domin gobensu da kuma muhallan aiki da zasu iya tsintar kansu nan gaba.

Menene manufar wannan shirin?

Mai taimkawa shugaban ƙasa ta ɓangaren labarai, Buhari Sallau, shine ya bayyana shirin gwamnatin a wata sanarwa da ya fitar a kafar sada zumunta Facebook.

A cewar Mista Sallau, manufofin wannan tsarin sun hada da:

"Inganta ɓangaren samar da ayyukan yi, gina matasa kan gudanar da aiki mai kyau da kwarewa a kan shugabanci, da kuma haɗa masu ɗaukar aiki da ingantattun ma'aikata."

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa wannan shirin na gwamnatin tarayya ya samu goyon baya da tallafin daga shirin samar da cigaba na UNDP.

A ranar Talata mai zuwa ake tsammanin shugaban ƙasa Buhari zai sanar da lokacin da matasa zasu fara neman amfana da shirin a hukumance.

Kara karanta wannan

Idan Bamu Yi Dagaske Ba Wataran Abujan da Muke Takama Ba Zata Zaunu Ba, Ministan Buhari

A wani labarin kuma Ministan Buhari Ya Bukaci Hukumar EFCC Ta Fara Bibiyar Gwamna Mai Ci Kan Badakalar Wasu Kudade

Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume, ya bukaci hukumar yaki da cin hanci EFCC ta fara bincikar gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.

Ministan ya kuma bukaci gwamna Ortom na jihar Benuwai ya fito ya baiwa shugaba Buhari hakuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel