Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong

Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong

  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya zargi wasu mutane da son ganin dawwamammen rikici ya barke a jihar Plateau
  • A wani jawabi da gwamnan yayi, ya ce mulkinsa ba zai taba barin bata-gari su tayar da fitina ba da sunan siyasa, addini ko kabilanci
  • A cewar gwamnan, dole a hada karfi da karfe wurin dakatar da wannan matsalar saboda yanzu haka jiharsa ta na shirin zama filin daga

Jos, Plateau - Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Plateau ya zargi wasu mutane da shirin samar da dawwamammen rikici a jiharsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a wani jawabi da yayi a jihar ta shi, gwamnan ya ce mulkinsa ba zai taba bari bata-gari su tayar da hankula a jihar ba da sunan siyasa, kabilanci ko kuma addini.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Gwamna Lalong ya zargi wasu mutane da son dawwamar da rikici a Plateau
Gwamna Lalong ya zargi wasu mutane da son dawwamar da rikici a Plateau. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dole mu yi da gaske wurin ganin mun yi aiki tukuru don dakatar da wannan tarzoma da ake shirin tayarwa,” a cewarsa.
Dukkan alamu sun nuna cewa akwai shirin kulle-kullen tayar da hankula da wasu mutane suke yi don cimma manufarsu. Kada mu bari su yi amfani da siyasa, addini ko bangaranci na yare wurin janye hankulan mu su yi ta’addanci.

Ya yi jawabin ne bayan kashe mazauna Yelwa Zangam guda 37 da aka yi.

Ga dukkan alamu, tsantsar ta’addanci kawai suke shiryawa kuma dole mu farka don kawo karshen hakan.
Duk da dai sun fara alakanta abin da yare da addini amma babu wani dalilin kashe rayuka. Mu mutane ne da muke bin dokoki kuma babu yadda za a yi mutum ya dauki doka a kansa duk tsanani duk runtsi,” a cewarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

Ya ku mazauna wannan jihar, mu yi amfani da fahimta, sasanci, tunani da dabaru wurin shawo kan ta’addanci komai girman tashin hankali. Duk wanda ya ki bin doka zai fuskanci fushin gwamnati don ba za mu taba barin a yi ta kashe-kashe da asarar rayuka ba.”

Gwamnan ya bayyana alhininsa game da yadda wasu suke amfani da addini, kabilanci da yare wurin cutar da mutane, Daily Trust ta wallafa.

Gwamna ya magantu kan shirin bude UNIJOS

Dangane da kara bude UNIJOS, gwamnan yace:

Ina so in yi amfani da wannan damar wurin tabbatar wa da iyayen daliban jami’ar Jos cewa muna kokarin ganin tarzomar ta kwanta don kada a sa rayukan yaransu a cikin hatsari.

Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce jami’an ta sun kwace bindigogi kirar AK-47 guda 25 da sauran miyagun makamai guda 6,460 cikin watanni 6 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

Punch ta ruwaito cewa, ya kara da bayyana yadda suka kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne guda 352 wadanda suke da masaniya da laifuka 221 daban-daban cikin wannan lokaci.

Jami’in hulda da jama’a, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya bai wa manema labarai a ranar Juma’a, inda yace tun daga watan Maris suke kamen har zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel