Zulum, Sarakuna, da Shugabannin Borno Sun Fadi Matakin da Zasu Dauka Kan Yan Boko Haram da Suka Mika Wuya

Zulum, Sarakuna, da Shugabannin Borno Sun Fadi Matakin da Zasu Dauka Kan Yan Boko Haram da Suka Mika Wuya

  • Shugabannin al'umma daga kowane ɓangare na jihar Borno sun gana kan mayakan Boko Haram da suka mika wuya
  • Taron wanda ya kunshi shugabannin siyasa, sarakuna da na addinai ya fidda matsaya kan lamarin
  • A sanarwar da suka fitar bayan taron, sun amince da tubabbun yan Boko Haram amma bisa wasu sharuddai

Borno - Shugabannin al'umma a jihar Borno, ranar Lahadi, sun amince a mai da mayakan Boko Haram da suka mika wuya cikin mutane, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Shugabannin sun amince da haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da gwamnatin Borno ta shirya domin tattauna matsalar tsaro da ake ciki a jihar.

Gwamnatin Borno ta tabbatar da cewa aƙalla yan kungiyar Boko Haram 3,000 ne suka mika wuya ga rundunar sojoji.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

Gwamna Babagana Umaru Zulum, wanda ya jagoranci taron, yace bayan mutum 3,000, akwai karin mutum 900 da suka mika wuya ga jami'an Kamaru.

Farfesa Zulum a wurin taro
Zulum, Sarakuna, da Shugabannin Borno Sun Fadi Matakin da Zasu Dauka Kan Yan Boko Haram da Suka Mika Wuya Hoto: The Governor of Borno state FB Fage
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum yace taron masu ruwa da tsaki ya zama wajibi ne biyo bayan yadda ake kace-nace kan yawaitar mika wuyan mayakan Boko Haram.

Zulum yace gwamnati tana bukatar saka masu ruwa da tsaki na jihar domin ɗaukar matakin da ya dace kan mayakan da suka aje makamansu.

Su waye suka halarci taron?

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da, manyan jami'an gwamnati daga mataki daban-daban, sarakuna, shugabannin addinai, jami'an tsaro da kuma wasu daga cikin mutanen jihar.

A karshen taron, sun tsaida matsayar amincewa da tubabbun yan ta'addan, amma sun bada sharuddan da za'a cika kafin mayakan su shiga cikin al'umma.

Legit.ng Hausa ta gano cewa sanarwar da suka fitar bayan taron tana ɗauke da sa hannun Antoni Janar na jihar, Kaka Shehu Lawan.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Wane sharudda suka kafa kafin amsar tubabbun?

Masu ruwa da tsakin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Borno cewa: "Su jagoranci lamarin mayakan da suka mika wuya da kulawa sosai kuma da bin ka'idoji da dokoki."

Taron ya jaddada bukatar "Bincike da ɗaukar bayanan mayakan Boko Haram domin gudun sako mutane masu hatsari cikin al'umma."

Hakanan shugabannin sun yi kira ga mazauna Borno "Su yi amafani da damar samun ilimi da gwamnatin Borno ta kirkiro musamman saka ƴaƴansu makaranta domin gudun kada a canza musu tunani."

A wani labarin kuma Ministan Buhari Ya Fallasa Yadda Ake Sata Ta Karkashin Kasa a Mulkin Shugaba Buhari

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yace koda ana sata a mulkin Buhari to sai dai ta karkashin kasa.

Yace amma a gwamnatin baya zaka ga mutum na wadaka da dukiya bayan ko shago ɗaya bai mallaka ba.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel