Kungiyar ASUU na shirin komawa yajin-aiki kwanan nan, ta ba Gwamnatin Buhari wa’adi

Kungiyar ASUU na shirin komawa yajin-aiki kwanan nan, ta ba Gwamnatin Buhari wa’adi

  • Malaman Jami’a su na iya tafiya yajin-aiki nan da wasu ‘yan kwanaki
  • Shugaban Kungiyar ASUU yace gwamnatin tarayya ta fara guje masu
  • Farfesa Emmanuel Osodeke ya zargi gwamnati da rashin cika alkawari

Kungiyar malaman jami’a na ASUU sun bayyana shirinsu na shiga wani sabon yajin-aiki. Hakan na zuwa ne bayan an rufe jami’o’i a kwanaki.

Punch ta kawo rahoto cewa kungiyar ASUU za ta shiga yajin-aiki ne a dalilin zargin da ta ke yi wa gwamnati na kin cika alkawarun da ta dauka.

ASUU ta ba Gwamnatin nan da gobe

ASUU ta ba gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari zuwa karshen wata (Talata, 31 ga watan Agusta, 2021), ta tuntube ta ko a rufe jami’o’i.

Jaridar tace sabon shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana mata hakan a lokacin da ta zanta da shi a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Yadda aka je har gida, aka maƙure babban ‘Dan Sanata Na Allah inji Gwamnatin Kaduna

A gobe wa’adin da malaman jami’o’in kasar suka ba gwamnatin tarayya zai kare, idan ba a cin ma matsaya ba, za a iya daina karantar da dalibai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farfesa Emmanuel Osodeke ya ke cewa wakilan gwamnatin tarayya sun daina daukar kiran wayarsu.

FUT Akure
Jami'ar Tarayya ta Akure Hoto: allafrica.com
Asali: UGC

Meyasa ASUU ta ke tunanin yin yaji?

“Gwamnatin tarayya ta ki tuntubarmu. Jami’an gwamnati sun daina. Kai, ba ma su daukar wayoyin salularmu yanzu idan muka kira su.”
“Mun sa hannu a yarjejeniya, kuma ko a watan Mayu, mun cin ma yarjejeniya ta karshe, yanzu an shigo Agusta, ba a cika alkawari ko daya ba."

Farfesa Osodeke yace kungiyarsu ba za ta ji nauyin shiga wani yajin-aiki domin nuna wa gwamnatin tarayya bacin ranta kan saba alkawari ba.

Har zuwa lokacin da muke tattara wannan rahoton dazu, gwamnatin tarayya ba ta yi magana game da zargin da kungiyar malaman suke yi mata ba.

Kara karanta wannan

Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane

A rufa mana asiri - Dalibai

Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu daliban jami’ar ABU ta Zaria da ba su dade da dawo wa karatu ba, a game da barazanar sabon yajin-aikin da yake yawo.

Wasu dalibai da suke ajin karshe a jami’ar sun fada mana ba su rokon a sake rufe makarantu, suka ce ba za su taba goyon-bayan a shiga yajin-aiki ba.

Kwanan nan ne Farfesa Osodeke ya gaji Biodun Ogunyemi a matsayin shugaban ASUU, ya cigaba daga inda ya tsaya a gwagwarmayarsa da gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel