Tsohon ministan Afghanistan da ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus

Tsohon ministan Afghanistan da ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus

  • Sayed Sadaat, tsohon ministan sadarwa na Afghanistan ya koma sayar da abinci a kasar Jamus
  • Bisa rahoton Reuters, bayan kwashe shekaru 2 a mukaminsa lokacin shugaba Ashraf, ya koma Jamus a watan Satumba
  • Yanzu haka Sadaat ya koma kai wa mutane abinci a gabashiin Leipzig, inda yake fama da caccaka iri-iri a kan aikin nasa

Jamus - Tsohon ministan sadarwa na Afghanistan, Sayed Sadaat ya koma sayar da abinci a kasar Jamus.

Kamar yadda ya bayyana a rahotannin Reuters, Sadaat ya bar kasarsa zuwa Jamus a watan Satumbar da ya gabata bayan kwashe shekaru 2 yana rike da mukaminsa lokacin mulkin shugaban kasa Ashraf Ghani.

Tsohon ministan Afghanistan da ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus
Tsohon ministan Afghanistan da ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ghani ya bar kasar a ranar 15 ga watan Augustan 2021, bayan Taliban sun amshi mulki, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

Ya tsere ta jirgin sama ya isa Tashkent da ke Uzbekistan daga nan ya wuce Dubai inda suka samar masa da mafaka saboda siyasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata tattaunawa da Reuters tayi da Sadaat, ya tabbatar da yadda ya koma sana’ar kai wa mutane abinci gidajensu a gabashin Leipzig, inda yace mutane da dama sun yi ta caccakarsa a kan zabar wannan aiki da yayi.

Babu abinda yake bani kunya,” kamar yadda mutumin mai shekaru 49 ya sanar da Reuters.
Ban damu ba! Don a baya na taba rike kujerar minista kuma yanzu ina yawon kai wa mutane abinci gida-gida. Duk aikin jama’a na ke yi.
Ina fatan sauran ‘yan siyasa za su cigaba da ayyuka da jama’a ba wai su yi ta boye-boye ba.”

Daily Trust ta ruwaito cewa, an samu rahoto akan yadda Sadaat ya dage yana neman aikin da zai dace dashi bayan ya isa kasar Jamus.

Kara karanta wannan

Rikicin Siyasa: Ina Nan Daram a Kan Kujerata, Shugaban PDP Ya Maida Martani

Yana da digiri a fannin sadarwa kuma yana fatan samun aiki a wani bangare mai yanayi da hakan.

Ina alfahari da yadda na ke aiki na, da na yi sata a matsayin minista da yanzu ina da miliyoyin dalolin da zan iya siyan gidaje ko otal a nan ko kuma a Dubai, kuma da yanzu bana bukatar neman aiki,” kamar yadda ya tabbatar a tattaunawar da aka yi da shi.
Amma ina farin ciki da yadda zuciya ta take a wanke ba na jin wata damuwa - ina yin aikina kamar kowa kuma ina fatan sauran ‘yan siyasa za su fara yi wa al’umma aiki ba wai su yita boye-boye ba.”

Tsohon ministan yana da takardun zama dan kasar Turai.

Kullum yana kwashe sa’o’i 4 a wata makarantar koyan yare da ke Jamus sannan ya kwashe sa’o’i 6 yana aikin kai wa mutane abinci a Lieferando,” kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Gwamnan jihar Benue ne sanadiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama

Obasanjo: Masu son ganin rabewar kasar nan makiyanta ne, za su ji kunya

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Juma’a ya ce yawancin makiyan Najeriya wadanda suke fatan rabewar ta ba za su ci nasara ba, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takarda wacce hadiminsa na harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya saki, ya ce Obasanjo ya ce kasancewar ‘yan Najeriya tare ya fi sauki a kan rabewarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel