Mutum biyu sun mutu, yayin da Sojoji suka ragargaji Yan bindiga suka kubutar da matafiya a Kaduna

Mutum biyu sun mutu, yayin da Sojoji suka ragargaji Yan bindiga suka kubutar da matafiya a Kaduna

  • Dakarun soji na Operation Safe Haven sun sami nasarar kuɓutar da wasu matafiya uku da motar su daga hannun yan bindiga
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun yi kokarin sace matafiyan ne a kan hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo
  • Hakanan wasu yan bindiga sun hallaka mutum biyu a wani hari da suka kai kauyen Makoro Iri, jihar Kaduna

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa rundunar sojin Operation Safe Haven sun kuɓutar da matafiya uku daga hannun yan bindiga a kan hanyar Gidan Waya-Godogodo, karamar hukumar Jema'a.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, a Kaduna.

Aruwan yace maharan sun yi awon gaba da matafiyan ne yayin da suka tare su a kan hanya, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan da Taliban ta karbe mulkin Afghanistan, Amurka ta kai hari da jirgi

Sojoji sun ceto matafiya a Kaduna
Mutum biyu sun mutu, yayin da Sojoji suka ragargaji Yan bindiga suka kubutar da matafiya a Kaduna Hoto: channesltv.com
Asali: UGC

Aruwan yace:

"Dakarun sojin sun yi gaggawar kai ɗauki bayan sanar da su, inda suka cimma yan bindigan kuma suka kuɓutar da mutanen."
"Hakanan dakarun sojojin sun kwato motar matafiyan da aka sace kirar Peugeot 307."
"Da yake martani kan rahoton wannan nasarar, Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya jinjina wa jami'an sojin bisa namijin kokarinsu."

Gwamnan ya kuma yaba wa sojojin bisa ɗaukin gaggawa da suka kai har aka samu nasarar kuɓutar da matafiyan, da kuma binciken da sojin ke gudanarwa a yankin.

Yan bindiga sun kashe mutum biyu

A wani harin na daban kuma, Mista Aruwan yace hukumomin tsaro sun kaiwa gwamnati rahoton cewa yan bindiga sun kashe mutum biyu a ƙauyen Makori Iri, karamar hukumar Kajuru.

Channels tv ta ruwaito cewa maharan sun farmaki kauyen inda suka harbe mutum biyu har lahira.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biyu

Aruwan ya kara da cewa gwamna El-Rufa'i ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan, tare da jimamin harin da aka kai kauyen Makoro Iri.

A wani labarin kuma Ida Ba Mu Yi Dagaske Ba, Wataran Za'a Kore Mu Daga Abuja, Ministan Buhari

Rotimi Amaechi , ministan sufuri, ya zargi wasu gurbatattun yan siyasa da kokarin tarwatsa albarkatun ƙasa, inda ya kara da cewa hakan yana da hatsari.

Tsohon gwamnan Rivers na tsawon zango biyu ya bayyana cewa karuwar matsalolin rashin tsaro ka iya shafar babban birnin kasar a kwana a tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel